Sports Betting

Trending

random

Dan wasan Super Eagles, Mikel Obi yayi sabon suna

 

– Kyaftin din Kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Mikel Obi ya canza sunan sa.

– Dan wasan na Kungiyar Chelsea Mike Obi, ba ya so ana bata masa suna.

Mikel

 

 

 

 

 

Dan wasan Najeriya, John Obi Mikel ya canza sunan sa ne saboda mafi yawancin mutane ba su iya kiran sunan daidai ba. Jaridar Mirror ta rahoto wannan labari. Yanzu haka dai dan wasan tsakiyan na Kungiyar Chelsea ta Ingila Mikel Obi (ko kace Mikel) ya koma Mikel John Obi.

KU KARANTA: MIKEL OBI NE KYAFTIN DIN NAJERIYA A OLYMPICS

Tun farko bai kamata ana kiran dan wasan na Super Eagles da suna ‘Mikel’ ba, dan wasan na Kasar Najeriya dai asalin sunan shi ne John Michael Nchekwube Obinna, sai dai an fi sanin sa da Mikel maimakon Micheal. Abin da ya faru tun fil azal shine, Kungiyar kwallo ta Najeriya (FA) tayi tuntuben rubuta sunan sa a matsayin Mikel, a maimakon Micheal tun shekaru goma sha uku da suka wuce. Da za aje gasar FIFA U-17 World Cup ne a shekarar 2013 Kungiyar kwallon Najeriyar ta bada sunan dan wasan a matsayin Mikel, tun wancan lokaci sai aka rika kiran sa da Mikel.

Dan wasan kuwa bai taba kokarin ya sauya sunan ba, yana son sunan, don haka aka cigaba da kiran sa Mikel, watau John Obi Mikel a Cheslea. Dan wasan ya kuwa koma Chelsea ni yau shekaru goma da suka wuce, tun a shekarar 2006, haka aka san sa da Mikel. Gudun wannan rikici dai ne, Dan wasan ya canza sunan sa zuwa Mikel John Obi yanzu.

KU KARANTA: MIKEL OBI NE KYAFTIN DIN NAJERIYA A OLYMPICS

A SAUKE MANHAJAR MU NA NAIJ.COM DOMIN A KARANTA LABARIN WASANNI.

The post Dan wasan Super Eagles, Mikel Obi yayi sabon suna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Dan wasan Super Eagles, Mikel Obi yayi sabon suna Reviewed by Olusola Bodunde on 04:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.