EFCC ta kama Dogara kafin ya sace komai- Jibrin
Dan majalisan wakilan tarayya , Abdulmumini Jibrin, yace babu lokacin da yakamata hukumar hana al mundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC ta bincike almundahanan biliyoyin kudi a majalisar wakilan tarayya.
Dan majalisan jihar Kano ya bayyana hakan ne a rananr asabar 13 ga watan Augusta ta shafin sadarwar sa ta Twita , ya bayyana cewa akwai almundahanan da akeyi a majalisar da dadewa kuma lokaci yayi da EFCC zata dau mataki a kai.
Jibrin ya tuhumci kakakin majalisa, Yakubu Dogara, da kuma wasu guda 3 akan yin amfanin da kafofin yada labarai domin bata masa suna. Dan majalisan ya nemi yan najeriya kwanaki da addu’an su akan abubuwan da yake fuskanta a cikin wannan yakin.
“Babu lokacin da ya kamata EFCC ta sake duba almundahanan biliyoyin kudi a majalisan wakilan tarayya da ya wuce yanzu. Dogara da saura suna ta kokarin yin amfani da kafofin yada labarai domin bata mini suna, ina kira dasu cewa da ma shirya gurfanr da zasuyi suke yi a maimakon haka Babu frofagandan kafofin yada labarai da zai dakatar dani. Kuma na ki sulhun cikin gida Dole ne mu gode ma kakaki dogara akan hakurin da ya baiwa yan najeriya akan karerayin ya dinga yi
“Wannan hakuri da bada, da yafi kakaki dogara ya kira taron majalisa ne yayi murabus. Wannan kakakin ne ya fada kwanakin baya yace aragizon kudi ba laifi bane kuma yafi karfin bincike. Ya fara jin zafi kenan.”
KU KARANTA : Jibrin ya kalubalanci Dogara kan mahawara gaban jama’a
A wata labara mai kama da haka, an samu wata sabuwar zance yayinda EFCC ke shirin damke Abdulmumini Jibrin kuma ta gurfanar da shi a kotu akan almndahanan kudi N17 Billion. Jibrin dai yace EFCC ta gayyace shi ne akan kare haske akan aragizon kasafin kudin da dogara da wasu 3 sukayi, amma ya kwashe sa’a 7 yana shan tambayoyi akan wasu zargi da ake masa
The post EFCC ta kama Dogara kafin ya sace komai- Jibrin appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us