Sports Betting

Trending

random

Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane

Sojojin rundunar hukumar sojan kasa ta 33 sun kama wasu mutane biyu Dayibu Abdullahi da Nasiru Adamu da ake zargin masu garkuwa da mutane a kauyen Badikko dake karamar hukumar Toro na jihar Bauchi.

An kama masu laifin da wata jaka dake shakare da kudi da suka kai naira dubu dari hudu da talatin da tara (N49,000,00) da sauran kayayyaki. Wata sanarwa da kaakakin rundunar soja Kanal Sani Kukasheka ya sanya ma hannu ya ce bincike ya nuna cewa kudin da aka kama a hannun barayin shine kason su na aikin sace wani mutum da suka yi a kwanan nan.

vllkyt3h50upvb885g.19c4e220

Kazalika an kama wani da ake zarginsa shima da yin garkuwa da mutane mai suna Jibrin Dakam a garin magama na cikin karamar hukumar Toro. Bincike ya nuna cewa Dakam ya tsere ne daga mabuyarsu dake dajin Burra biyo bayan wani samame da sojoji suka kai a dajin.

A wani labarin kuma, jami’an sojin runduna ta 33 sun kaddamar da samame da hare hare a a jihar Bauchi don kakkabe ragowar yan fashi biyo bayan kiraye kiraye da koke koke da al’ummar jihar sukayi.

da wannan ne rundunar ta fara wani sintiri a ranar 21 ga watan agusta a tsakankanin garuruwar Dutsen Mairama da Dogon ruwa duk a cikin dajin Burra na kananan hukumomin Toro da Ningi. A yayin karanbattan an kashe masu garkuwa guda uku sa’annan an an lalata sansaninsu, daga bisani aka kwashe makamai da dama daga sansanin.

The post Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane Reviewed by Olusola Bodunde on 02:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.