‘Yan wasan Manchester da ake shirin sallama
– An taya ‘yan wasan Manchester City.
– Wata Kungiya a Ingila na neman Golan Manchester City, Joe Hart.
– Ana zawarcin W. Bony, Sami Nasri da kuma Eliquim Mangala.
– Bredan Rodgers na neman Batian Schweinsteiger na Manchester United.
Kungiyar Manchester City na kokarin sakin yan wasa kusan 4 kafin a rufe kasuwar cinikin yan wasa.
Manchester City za tayi kokarin ganin ta salami ‘yan wasan da ba ta bukata kafin a rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa na Turai, za a rufe kasuwar ne a daren 31 ga watan Agustan nan.
Ga wasu daga cikin yan wasan da ake kokarin sallama:
Joe Hart
Everton da makwabtan su Liverpool suna zawarci Golan Ingilan, bayan da Koci Pep Guardiola ya bayyana cewa dan wasan na iya tafiyar sa. Claudio Bravo, Golan Barcelona ya iso Kulob din na Manchester City domin ya kammala komo buga masu.
Wilfried Bony
Kungiyar West Ham na neman dan wasan Gaban nan Wilfried Bony, Kungiyar tana kokarin sayen dan wasan musamman bayan ta nemi dan wasa Carlos Bacca na Kasar Columbia, amma abin bai yiwu ba.
KU KARNTA: CLAUDIO BRAVO YA ISO MANCHESTER
Samir Nasri
Sami Nasri na shirin barin Manchester City, ana ganin cewa dan wasan zai koma Kungiyar Besiktas, Manchester City na yunkurin saida tsohon dan wasan na Arsenal.
Eliaquim Mangala
Kungiyar Napoli ta Serie A club na neman a ba ta aron dan wasan bayan nan, Eliaquim Mangala. Dan wasan na Kasar Faransa ya koma benci tun zuwan John Stones daga Everton wannan shekarar.
Bastian Schweinsteiger
Haka kuma, Kocin Kungiyar Celtic Brendan Rodgers, na neman da wasan tsakiyar nan na Manchester United, Bastian Schweinsteiger. Tsohon dan wasan na Bayern Munich mai shekaru 33 ya shiga wani tsaka-mai-wuya tun da Jose Mourinho ya dawo kungiyar ta Manchester United.
The post ‘Yan wasan Manchester da ake shirin sallama appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Post Comment
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us