Arsenal: Joel Campbell ya koma Sporting Lisbon
Dan wasan Arsenal na gaba, Joel Campbell ya koma kungiyar wasa ta Sporting Lisbon da ke kasar Portugal.
Arsenal
Campbell din dai zai zauna a Lisbon ne har zuwa karshen kakar wasa ta bana. Dan wasan mai shekara 24 ya kwashe shekara biyar a Arsenal amma kuma yana ta son ya koma babban kulob.
Ya ci wa Arsenal kwallaye hudu a wasanni 30 na kakar wasan da ta gabata. Campbell, dan asalin kasar Costa Rica ya je kungiyoyi a kan aro kamar Lorient da Real Betis da Olympiakos da kuma Villareal.
The post Arsenal: Joel Campbell ya koma Sporting Lisbon appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Arsenal: Joel Campbell ya koma Sporting Lisbon
Reviewed by Olusola Bodunde
on
02:45
Rating:
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us