Zan kara sayo ‘yan wasa – Wenger
Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ya shirya kara sayo wasu ‘yan wasan tamaula kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a ranar 31 ga watan Agusta.
Wenger na shan suka kan kin sayen fitattun ‘yan wasa a shekara da dama, da kuma fama da yawan rauni da ‘yan kwallon Arsenal ke yi. Babban dan kwallon da Wenger ya saya a bana shi ne Granit Xhaka, wanda aka dauko daga Borussia Monchengladbach kan kudi fan miliyan 34.
A wasan da Arsenal ta yi rashin nasara a hannun Liverpool da ci 3-4, sai sauya Aaron Ramsey da Alex Iwobi aka yi a karawar sakamakon rauni da suka yi. Tun kafin a fara kakar wasannin bana Per Mertesacker da Gabriel da kuma Jack Wilshere suna jinyar rauni tare da Danny Welbeck.
Wenger ya ce a shirye yake ya sayo dan kwallo ko nawa ne kudinsa, matsalar ita ce ba za ka samu irin dan wasan da kake bukata ba.
The post Zan kara sayo ‘yan wasa – Wenger appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us