Sports Betting

Trending

random

Buhari yayi Magana kan abunda yan arewa sukayi

-Kare da aka sanya ma suna Buhari ya haddasa cece kuce a tsakanin yan Najeriya

-Chinakwe mamallakin Karen yace shi ya aikata abunda yayi saboda soyayyarsa ga shugaban kasa Buhari

-Dan shekara 40 yace yan arewa mazauna gurin da yake sun san wani abu game da mutuwar Karen sa

Kimanin kwanaki biyu da suka wuce, an kama wani dan kasuwa mai suna Chinakwe a jihar Ogun saboda ya sanya wa karensa sunan shugaban kasa Buhari.

Joe Foertemose Chinakwe, wanda ke aikin siye da siyarwa, yace yana hutawa tare da iyalinsa lokacin da daya daga cikin makwabtan sa daga jumhuriyyar Nijar ya tambaye shi kuma yake neman bayani daga gare shi kan dalilin da yasa ya yake kiran karensa da Buhari.

Joe Fortemose Chinakwe

Dan kasuwan mai shekaru 40 yace tambayar da makwabcin nasa yayi masa ne yayi sanadiyar kai shi bayan kanta a ofishin yan sandan Eleweran a jihar Ogun.

KU KARANTA KUMA: Yan sandan Najeriya sun hana taron bikin aure a kano

An saki mutumin sakamakon sanya baki da sarkin Hausawa da shugaban yan cirani na jihar gabaki daya sukayi cikin lamarin. Bisa ga jaridar Vanguard mutumin ya bayya dukkan aihanin abubuwan da suka faru game da al’amarin.

Ya kuma bayyana cewa a lokacin da yake ofishin yan sanda an umarce shi da yaje ya zo da Karen, ya yarda kan cewa zai je ya taho da shi amma kafin ya kai gida, yace yaje ya tarar yan arewa dake zama a unguwarsu sun hadu sun kashe Karen.

The post Buhari yayi Magana kan abunda yan arewa sukayi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Buhari yayi Magana kan abunda yan arewa sukayi Reviewed by Olusola Bodunde on 05:17 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.