Shugaban kasa Buhari ya tarbi Fasto Bakare a fadar sa (Hotuna)
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hadu da Fasto Tunde Bakare a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a 19 ga watan Augusta.
Fasto Bakare ya isa fadar shugaban kasa da misalign karfe 2.45 na rana a agogon gida Najeriya kuma ya tafi Ofishin shugaban kasa kai tsaye domin wani gamuwa na sirri. Bayan gamuwar da ya kai kimanin sa’a daya, Fasto Bakare ya nuna jin dadinsa kan lafiyar shugaban kasa amma duk da haka bai fallasa manufarsa na ziyarar ba.
A safiyar ranar anyi rahotanni game da gamuwar sirri da shugaban kasa yayi tare da Yakubu Dogara, kakakin majalisar wakilai.
KU KARANTA KUMA: Shugabannin APC na kudu maso yamma sun nace a kan sake fasalin al’amura
Masu nazarin siyasa sun zaci cewa ziyarar na da alaka da sabanin dake cikin majalisar dokokin da kuma tattaunawa kan dangantakar dake tsakanin yan majalisar zartarwa da yan majalisar dokoki na gwamnatin tarayya, bayan zargi kan arigizon kasafin kudi na shekara 2016.
A Kwanakin baya munji cewa shugaban kasa Muhammadu buhari da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara sunyi wani ganawa na sirri a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja. Dogara ya isa ofishin shugaban kasa domin gamuwar na sirri da misalign karfe 2.30 na ranan.
The post Shugaban kasa Buhari ya tarbi Fasto Bakare a fadar sa (Hotuna) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us