Dalung ya biya yan wasan olimfik alawus din su
Ministan wasanni Solomon Dalung ya sanar da biyan yan wasan Najeriya dake wakiltar kasar a gasan Olimfik dake gudana a kasar Rio ta Brazil kudin alawus dinsu kimanin $47, 850, kwatankwacin naira miliyan 16 da 700,000.
A wani sanarwa da Dalung ya fitar a ranar Laraba, yace gaba daya yan wasan kwallo na kasa da shekaru 23 sun amshi alawus dinsu na kwanaki 11 da suka kwashe a sansanin atisaye, inda aka biya kowanne daga cikinsu $1,650, kimanin N,557,000. Ma’ana an biya kowanne dan wasa $150 kenan a kowane rana da yake a sansanin atisaye tun bayan nasarar da suka samu a karawarsu da kasar Sweden a ranar Litinin.
Dalung yace an biya yan wasan ne da masu horar dasu kudadensu kai tsaye don su kasance masu kara kwazo a kan aikinsu, da kuma samun kwarin gwiwa. “alawus din ku na zaman sansanin atisaye a lissafe yake kuma a kasafce yake. Babu sauran bayar da tatsuniya game da kudadenku. Zaku samu dukkanin alawus dinku tare da hakkokinku, don bamu san abin da zai zame maku tarnaki” inji Dalung. “muna so ku fuskanci abin da ya kawo ku. Kun riga kun nuna ma duniya cewa ku ba kanwar lasa bane, kun nuna zaku iya lashe gasar, duk da irin kalubale da kuke fuskanta. Babu sadaukarwar da ya wuce wannan.”
Kungiyar kwallon kafa ta yan kasa da shekaru 23 mai suna Dream Team zata fafata da kasar Columbia a wasan karshe na rukunin B a ranar Laraba 10 ga watan agusta. Kungiyar ta samu tsallakawa zagaye na biyu bayan ta lallasa Japan 5 da 4 a wasan ta na farko, kuma ta buge kasar Sweden ci 1 da babu a wasa na biyu.
The post Dalung ya biya yan wasan olimfik alawus din su appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us