Sports Betting

Trending

random

Najeriya ta samu cin kyauta a Gasar Olympics

Allah yayi: Najeriya ta samu cin kyauta a Gasar Olympics.

Kungiyar Dream Team VI ta Najeriya ta samu cin kyauta a Gasar Olympics na RIO 2016. Kungiyar kwallon kafar kasar ta doke Honduras da ci 3-2 a wasan tatance na uku a Gasar ta Olympics, hakan ya sa Najeriya ta samu lashe kyautar tagulla a Gasar.

DreamTeam defeated Honduras to win bronze at Rio Olympics

Dan wasan gaban Najeriya, Sadiq Umar ya fara bude ragar a minti na 34, dan Aminu Umar kuma ya kara ta biyu bayan an dawo hutun rabin lokaci. Kafin kace mene kuma, dan wasa Sadiq Umar ya kara lekawa. Sai dai dan wasa Anthiny Lozano ya ci wa Honduras kwalla guda a wajen Minti na 70. Marcelo Pereira ya ci ta biyu ana kusa da hura tashi wasa, hakan ya sa wasan ya kai 3-2, Honduras ta budawa Najeriya wuta a wannan yanayi. Sai dai kuma bakin alkalami ya riga ya bushe, Kasar Najeriya ta yi nasara, aka tashi da ci 3-2, Najeriya ta kuma samu kyautar tagulla.

Najeriya dai ta take wasan ne da ‘yan wasa: Daniel, Sincere, Shehu, Ekong, Aminu Umar, Imoh Ezekiel, Mikel (C), Sadiq Umar, Azubuike, Amuzie, da kuma Usman Muhammed. An fara wasan ne a Karfe 5 na Yamma (Agogon Najeriya). Kasar Jamus ce dai ta hana Najeriyar zuwa wasan karshe a Gasar inda ta dura mata ci biyu da nema don haka suka sha alwashin lashe kyautar tagulla a wasan. Yan wasa irin su Azuibuke sun dawo cikun Kungiyar an taka da su bayan ya rasa wasan Jamus.

Honduras kuwa wanda sune takwaran Najeriya sun sha uban ci wajen Brazil, inda su Neymar suka lallasa su har ci shida da ba ko daya. An buga wannan wasa ne a filin Maracana Stadium, Birnin Rio de Janeiro, a Kasar Brazil

KU KARANATA: DALILAN DA YA SA AKE DOKE NAJERIYA

The post Najeriya ta samu cin kyauta a Gasar Olympics appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Najeriya ta samu cin kyauta a Gasar Olympics Reviewed by Olusola Bodunde on 06:34 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.