Sports Betting

Trending

random

Nijar ta hana Najeriya zuwa Gasar AFCON U-17

 

– Kungiyar Golden Eaglets ta sha kashi da ci har 3-1 a Birnin Niamey na Jamhuriyar Nijar.

– An dai fatattaki mafi yawon yan wasan Kungiyar bayan an gano cewa sun yi kagen shekaru.

– Najeriya ba za ta je Gasar U-17 AFCON na Nahiyar Afrika ba a shekarar mai zuwa.

Shocker! Nigeria U17 knocked out of AFCON

Kungiyar Golden Eaglets ta Najeriya ta sha kashi hannun Jamhuriyyar Nijar, kenan ba Kasar ba zuwa Gasar AFCON na Shekarar 2017.

Golden Eaglets ba za su je Gasar Zakarun Nahiyar kwallon kafar kwallon kafa ban a shekara mai zuwa, za a buga Gasar na AFCON na U-17 (wanda ba su wuci shekaru 17 ba) ne badi. Najeriya dai ba za ta samu zuwa ba bayan ta sha duka hannun Jamhuriyar Nijar jiya, Asabar 20 ga watan Agusta.

KU KARANTA: PELE ZAI ZO NAJERIYA

Nijar ta ci Najeriya ne kwallaye har uku, sai dai Najeriyar ma ta samu jefa kwalla daya tal. A zagayen farko Najeriya ce tayi nasara kwanaki da ci 1-0, sai dai yanzu reshe ya juya da mujiya, an zubawa Najeriyar ci 3-1 a Birnin Niamey.

Wannan ne karo na farko a Tarihi da Kasar ba za ta buga dukkanin wasannin cin kofin Nahiyar ba watau na AFCON. Ko ga Kungiyar Super Eagles ta Kasar, ita ma ba za ta je Gasar ba a Kasar Gabon shekarar badi ta 2017, haka kuma Kungiyar Flying Eagles ba za ayi ba su ba a Sudan. Ga kuma ‘yan U-17 na Golden Eagles.

Bincike dai ya nuna cewa mafi yawan yan wasan U-17 na Najeriya har fiye da guda 26 sun wuce shekara 17, hakan ya sa aka cire su daga Kungiyar. An dai yi amfani da Fasahar gwaji na MRI da ke duba jikin mutum. ‘Yan wasan na U 17 din Najeriya ne kadai wadanda suka taba cin Kofin Gasar Duniya har sau 5 a tarihi

 

 

The post Nijar ta hana Najeriya zuwa Gasar AFCON U-17 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Nijar ta hana Najeriya zuwa Gasar AFCON U-17 Reviewed by Olusola Bodunde on 06:34 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.