Premier League: Chelsea, Tottenham da Everton sun samu nasara
– Chelsea ta doke Watford bayan an fara cin ta.
– Tottenham da ma Hull City sun ci wasan su.
– Burnley sun ba Liverpool mamaki.
– Arsenal da Leicester City an yi cangarasa.
Ahmed Musa na Leicester City kenan da kuma dan bayan Arsenal, Hector Bellerin a fafatwar su wannan mako a Gasar Barclays Premier league. An tashi wasan 0-0.
Chelsea sun samu nasara bayan da kuwa su aka fara ci a wasan su da Kungiyar Watford a gidan Vicarage road. Chelsea ta samu cin 2-1 a wannan wasa ta hannun sabon dan wasa Michy Batshuayi da kuma Diego Costa. Dan wasa Capoe ya fara cin Chelsea bayan an dawo hutun rabin lokaci.
Sai dai kuma su Liverpool sun sha mamaki wajen Burnley. Sababbin shigowar na Premier league sun sha kashi hannun Burnley har gidan Anfield. Sam Vokes na Kasar Wales ya ci kwallo ana fara wasan, kafin a tashi kuma Andre Gomez ya kara.
Tottenham kuma tayi nasara a wasan ta da ta buga mai zafi da Crytsal Palace gidan ta na White Hart Lane. Vincent Wanyama ne wanda ya ci kwallo a wasan. Wani abin mamakin kuma shine, Kungiyar Hull City ta kara samun nasara a wasan ta da je bakunci gidan Swansea da ci har 2-0. Kungiyar Hull City ta ci wasanni biyu kenan. Maloney da Abel Hernandez suka jefa kwallayen lokacin da aka kusa hura usir.
Everton ta doke Wes Brom, wanda har yau ba ta samu ta ci wasa ko daya ba. Miralas da Gareth Barry suka ci kwallayen bayan da Macauley na Wes Brom din ya jefa kwallaye guda da fari. Arsenal sun tashi da Leicester babu ci a Gidan King Power, har yanzu dai cikin su babu wanda ya ci wasa ko guda a Gasar na Premier league.
KU KARANTA: JOE HART ZAI BAR MAN CITY?
The post Premier League: Chelsea, Tottenham da Everton sun samu nasara appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us