Rikicin PDP: Babu ruwana – Atiku ya maida martani ga masu sukarsa.
_ An hanko cewar rikicin PDP baya da karshe.
_ Anata nunama sanannun yan siyasa yatsa dacewar suke rura wutar da Jam’iyar adawa ta farko a kasannan ke fuskanta.
Tsohon shugaban kasan Najeriya Atiku Abubakar yace bayida masaniya akan matsalar da babbar Jam’iyar Afirka ada wato PDP ke fuskanta. Wanda ya taba zama mutum na biyu a Najeriya ya bayyana abunda ya sani akan rikicin PDP dake faruwa a yanzu.
A ranar Lahadi 21 ga watan Agusta, haifaffen dan Adamawa kuma jigon dan siyasa a jam’iyar APC yayi watsi da kagen dake yawo a jaridu cewar yana da hannu akan rikicin shugabancin dake gudana akan jam’iyar datayi mulki ada.
Atiku yayi Magana bisa cibayan rahotannin wata jarida mai suna Independent NGR, wanda ta bayyana a shafinta na Tweeter, yace baida masaniya akan rikin PDP dake gudana a halin yanzu. Tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriyan baiji dadin labarun dake nuna yanada hannu acikin hargitsin PDP ba, A inda ya mayar da martani da wani dan bayani a shafinsa na musamman na Tweeter, mai suna AtikuOrg.
Ga abunda aka gani a shafinsa na Twitter; Yake IndependentNGR, tsohon mataimakin Shugaban kasa wato Atiku, baida hannu a rikicin PDP. Akwai hasashen dake nuna cewa gwamnonin PDP da masu fada aji na jam’iyyar sun nuna cewa Atiku ne abun dogaran da zai iya kwato masu mulki daga APC a 2019.
The post Rikicin PDP: Babu ruwana – Atiku ya maida martani ga masu sukarsa. appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us