Suarez da Messi sun dagargaza Real Betis
– Kungiyar Barcelona ta fara wasan La-liga da gagarumar nasara bisa Real Betis.
– Lionel Messi da Suares kadai sun jefa kwallaye biyar a wasan.
– Ruben Castro ya samu ya jefawa Kungiyar tasa ta Betis kwallo a wasan.
Dan wasa Luis Suarez yaci kwallaye uku, inda kuma dan wasa Lionel Messi ya jefa biyu a wasan Kungiyar da Real Betis. Barcelona tayi nasara da ci 6-2.
Barcelona ta fara wasan Gasar La-liga na Kasar Spain da gagarumar nasara, Kungiyar ta ba Real Betis mugun kashi a filin wasa na Camp nou. Barcelona dai ta zubawa Betis ci har 6-2 a wasan. Ana fara wasa Arda Turan ya jefa kwallon farko cikin minti shida, nan take Ruben Castro ya ramo, kamar da gaske. Castro ya ci wata firinkit ne kuwa.
Dan wasa Lionel Messi ya shimfida wata kwallo a cikin raga, kafin a tafi hutun rabin lokaci kuwa har Luis Suarez ya kara guda. Bayan an dawo kuwa, Dan wasa Messi ya kara cin wani kwallon nesa daga ragar. Lionel Messi dai bai gaza ba, ya mikawa Luis Suarez ya kara ta biyu shima, ta biyar kenan a wasan.
KU KARANTA: YAN WASAN DA GUARDIOLA YA TABA SAMU MATSALA DA SU
Abin bai kare ba, Luis Suarez ya buga wata firinkit shima har raga ya cika kwallaye uku a yinin watau hatrick kenan. Sai dai dan wasa Castro ya kara ta biyu shima kafin a tashi. Barcelona dai tayi nasara da ci 6-2 a wasan na farko na Gasar La-liga 2016/17.
The post Suarez da Messi sun dagargaza Real Betis appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us