Buhari Ya Kara Soke Wani Aikin Jonathan
Karatu a Kwalejin ilimi ta Kano ya tsaya cik saboda Malamai na yajin aikin akan canza shawarar da gwamnatin Tarayya tayi akan daga darajar makarantar zuwa Jami’ar ilimi ta Tarayya.
Gab da lokacin hannunta mulki, zauren gudanar na kasa (FEC) ya bada umurnin daga darajar makarantu guda 3 domin su kara samar da ilimi.
Shugaban kungiyar Malamai masu karantarwa Dacta Abubakar Sadiq Haruna ya bayyana cewa gwamnati bata barsu da wata dama ba illa su umurci Ya’yan kungiyar su tafi yajin aikin sai har sabuwar gwamnatin ta dawo da shawarar ta ta.
Sannan kuma yayi Allah wadai da wannan canza shawara da sabuwar gwamnatin tayi. Yace canjin shawarar ba zaya haifar da Da mai ido ba.
Dacta Abubakar ya bayyana cewa makaranatar da alfahari da gine ginan dake gare ta kamar dakunan karatu, da wajajen zama, sannan kuma wasu aikace aikace na zan zuwa.
Sannan ya roki daliban makarantar dasu goyi bayan abunda malaman sukayi.
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post Buhari Ya Kara Soke Wani Aikin Jonathan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us