Dalilin Da Ya Sanya Jonathan Kawai Za’a Bincika
John Oyegun, Shugaban Jam’iyyar APC ya bayyana cewa Shugaba Buhari gwamnatin Jonathan kawai zaya bincika banda na baya.
Shugaban Jam’iyyar ya bayyana cewa binciken za’a yi shine domin a gano iya barnar data auku shekaru 6 da suka wuce. Ya bayyana haka ne a wata fira da yayi da Jaridar Daily Independent.
Yace: “A yanzu shekaru 4 banda watanni 2 suka rage ma shugaba Buhari. Idan akace bincike za’ayi, daga ina za’a fara? Shekaru 16? Ko kuma shekaru 50 da suka wuce?. Ni ba zani iya yin magana da yawun shugaba Buhari ba. Kuma ba zani iya magana da yawun fadar shugaban kasa na.”
Shugaban kuma ya bukaci yan Najeriya su ba shugaban kasa lokaci domin yayi aiki. Yace: “Kwana 100 watanni 3 ne kawai, idan gwamnati ta daidaita, komai za yayi kyau.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post Dalilin Da Ya Sanya Jonathan Kawai Za’a Bincika appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us