Yan Sanda Sun Kama Matasa Yan Fashi Da Makami
Yan sanda sun kama wasu yan makaranta wandanda ake zargin yan fashi ne a Legas. Wadanda ake zargin sune Peter dan shekara 18, da Emeka dan shekara 19.
An kama su ne a unguwar Agbado a Jihar Legas.An kama wadanda ake zargin ne bayan da suka shiga wasu shaguna suka dauki Wayoyin Salula da kayan sawa.
A halin da ake dai suna nan anayi masu tambayoyi a Ofishin hana fashi da makami na kasa (SARS) dake Legas. Wadanda ake zargin sunyi ikirarin cewa wannan shine karon su na farko. ” Munyi hakan ne saboda bamuda kudi tun bayan da muka gama makarantar sakandare” cewar matasan.
Peter yace: “Na rubuta jarrabawar shiga jami’a, ina jiran abani damar shiga ne. Nayi aikin Leburanci a wata ma’aikata wanda acan ne na dahu da Emeka.
“Ina so inyi kudi ne da wuri sai ya sanya na jawo Emeka. Akwai shaguna da yawa wajen hanyar AIT Agbabado, wasu basu kulle shagunan su sosai.”
Daga wajen Emeka, shi kuma cewa: “Abokan banza ne suka tunzura ni. Dani Lebura ne kuma na gode Allah. Yanzu gashi ya tunzura ni cikin matsala.”
Note: There is a poll embedded within this post, please visit the site to participate in this post's poll.The post Yan Sanda Sun Kama Matasa Yan Fashi Da Makami appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us