Babban Hotuna Daga Kabarin Shehu Usman Danfodiyo
Wakilin Naij.com Abdulbaqi Jari yayi tattaki zuwa kabarin Shehu Usman Danfodiyo inda ake cema “Hubbaren Sheu.” Shin yaya wajen yaki?
Hubbare ko Hubbaren Shehu Usman Danfodiyo na cikin garin Sakkwato ne. Tana nan kusa da Masallacin Shehu, kusa da fadar Sarkin Musulmi.
Hubbaren Shehu babban waje ne inda aka birne Shehu Danfodiyo wanda yayi Jihadi a 1804. Anan Hubbaren, Shehu Danfodiyo na nan birne tare da wasu daga cikin ya’yan shi da kuma sojojin shi. Daga gafe kuma akwai sauran iyali da jikoki hadda mariganyi Sarki Musulmi Muhammadu Maccido wanda ya rasu a cikin hadarin jirgin sama a 2006.
Daga fari dai idan mutum ya isa wajen zaya iske mutane a zaune a wajen suna neman sadaka. Kafin mutum ya shiga koda farko sai ya cire takalman shi. Akwai yan sanda zaune a gafe suna gadin wajen. Sai mutum ya shiga wani dogon zaure wanda ya kusa yadi 200. Zaya isa wani zaure inda zaya iska wanda suke kira wakili. Duk inda mutum yaje dole sai ya bada sadaka.
Idan mutum ya shiga kwaryar inda aka birne Shehu, dan rakiyar nashi zaya bukaci shi yayi addu’a. Idan mutum ya gama sai ya fita za’a nuna ma mutum kabarin Aliyu Jedo wanda shi kwamandan Shehu ne. Daga bisani kuma mutum zaya shiga inda aka birne Nana Asma’u. Sai kuma wajen su Hassan Dan Mua’zu da sauran matan Shehu. Idan mutum ya gama duka, sai ya fita ya shiga wata kofa inda zaya je wajen Sarkin Muhammadu Maccido, domin shi daban aka birne shi.
Abun mamaki ne kuma abun takaici akan yadda aka bar wajen ya lalace. Wani waje ma za kaga rufin gyara ta cinye shi yana neman fadowa.
Akwai bukatar ma’aikatar al’adu data addini na Sakkwato su gyara wajen. Sannan kuma akwai bukatar a wayar na mutane da kai game da masu zuwa suna rokon sa’a a wajen domin addinin musulunci ya nuna cewa sa’a a wajen Allah.
Ga babban hotuna daga ziyarci kabarin Shehu Usman danfodiyo a kasa:
The post Babban Hotuna Daga Kabarin Shehu Usman Danfodiyo appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us