Sports Betting

Trending

random

Jonathan Bai Iya Tsawata Ma Diezani – Agbaje

Wani fitaccen Lauyan kundun tsarin mulki wanda ke zaune a Legas, Fred Agbaje ya bayyana cewa tsohon Shugaban Kasa Jonathan ya Kasa tsawata na Diezani Alison-Madueke saboda taba da tayi karfi sosai.

Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan da Tsohuwar Ministan Mai Diezani Alison-Madueke

A wata Fira da Agbaje yayi da jaridar Daily Independent, Agbaje ya bayyana cewa:
“Diezani ta samu karfi sosai har ta kai ga tsohon shugaban kasa Jonathan baya Iya tsawata mata. Saboda karfin ministocin daya nada sai ya zama baya Iya yi masu komai.”
A cewar Agbaje, wannan yaki da rashawa da Shugaba Muhammadu Buhari yake yi ya nuna cewa dagaske yake wajen yin yaki da rashawa a fadin tarayyar Najeriya.
Lauyan na kundun tsarin mulki ya bayyana cewa wannan zaya zama misali ha sauran wadanda sukayi ta’ammali da rashawa cewa hannun doka ba zaya Kyale su ba.
Lauyan kuma yayi kira ga ma’aikatan gwamnati dasu kaucema rashawa a cikin aiyukan su. Lauyan ya bayyana cewa wadanda ke cikin gwamnati a Yanzu su San cewa lokacin yin abunda bai dace ba ya wuce. Dole ne yayi abunda ya kamata a yanzu.

The post Jonathan Bai Iya Tsawata Ma Diezani – Agbaje appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.


Jonathan Bai Iya Tsawata Ma Diezani – Agbaje Reviewed by Olusola Bodunde on 04:57 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.