Tsagerun Nija Delta Sun Badi Gargadi Akan Gwamnati
Kimanin tsofaffin tsagerun Nija Delta 500 a karkashin (PAP) suka bada gargadi akan idan ba’a biya su kudin su Na Wata 3 ba zasu tada fitina a yankin.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, sun bayyana cewa zasu keta alkawarin idan har Janar Boroh bai biya su kudaden su ba a cikin kwana 5.
Inda suke magana a Yenagoa, jihar Bayelsa a ranar Litinin 26, ga watan Oktoba, sun bayyana cewa zasu kulle hanyar East-West Wanda itace babbar hanyar shiga kudu maso kudu.
Bapilede Enere, daya daga cikin wadanda abun ya shafa ya bayyana cewa an biya wasu kudaden su, amma sama da 500 ba’a biya su ba.
“Har yanzu dai basu ce mana komai ba. Wasu an biya su Na Wata 2. Amma mu har yanzu muna jiran a biya mu. Kwana kin baya wasu sunyi zanga-zanga a Abuja inda suka bukaci a biya su kudaden su wadanda ba’a biya ba. Sun zargi Peter Evah da almundahana da sama da Miliyan 405.”
The post Tsagerun Nija Delta Sun Badi Gargadi Akan Gwamnati appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us