Abubakar Audu Ya Rasu
Tsohon gwamnan jihar Kogi da kuma dan takarar gwamna jam’iyyar APC, Dan Sarki Abubakar Audu ya rasu. Gidan jaridar ma Sahara Reporters ta fara fitar da labarin a lokacin da aka bayyana cewa babu wanda ya ci zaben.
Wakilin Naij.com ya garzaya gidan shi a karamar hukumar shi dake Ofu. Amma sai aka fada mashi cewa ya far wajen.
Haka zalika a shafukan sada zumunta ma mutane nata tattauna akan batun, inda wasu suka ce karya ne. Amma Sai dan jaridar nan Dele Momodu ya aika da Wani saki yace: “Babban labari daga jaridar The Boss. Mun samu labari daga Dangin Abubakae Audu cewa ya rasu.”
Wani na kusa da Audu wanda baya so a bayyana sunan sa ya fada ma jaridar Premium Time a cewa lallai Audu ya rasu.
Hukumar zabe ta kasa ta bayyana cewa jam’iyyar APC ya samu kuri’u 140,867, ita kuma PDP Ta samu 199, 514, amma babu wanda yaci zaben sai an sake.
The post Abubakar Audu Ya Rasu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
Abubakar Audu Ya Rasu
Reviewed by Olusola Bodunde
on
01:33
Rating:
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us