Hatsari ya lalata Mota 6 a Abuja
– Hatsarin ya lalata Motoci 6 a Abuja
– Hatsarin ya auku ne saboda rashin biyayya ga dokokin hanya
– Babu wanda ya rasu a ciki
Wani mummunan hatsarin mota ya auku a garin Abuja, Area II a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris, Naij.com ta ruwaito.
KU KARANTA: Layin mai zaya kare nan da kwana 2 – Kachikwu
Masu bada agajin gaggawa basu iso ba lokacin da akayi hatsarin sai dai mutane ne suka bada agaji. Hatsarin mota ya yawaita a Najeriya ne saboda rashin kyawun hanya, rashin lafiyar motoci da kuma rashin bin dokokin tuki.
Ga Hotunan:
Shugaba Buhari zaya tafi Malabo
Akwai hukumomi da yawa wadanda suke da alhakin kula da lafiyar hanya da kuma ababen hawa. Akwai hukumar Federal Road Safety Commission (FRSC), wadanda suke da hakkin kula da hanyoyin gwamnatin tarayya. Akwai kuma Vehicle Investigation Officer (VIO), wadanda suke da hakkin kula da lafiyar ababen hawa.
Bincike ya nuna dubunnan mutane ke mutuwa sakamakon hatsarin mota a kowacce shekara a Najeriya. Wannan kuma na karuwa ne saboda rashin samuwar agajin gaggawa ga wadanda suke raunta suke zubar da jini.
Wasu kuma na ganin cewa bama yara kanana motoci saboda iyayen su nada hali shima yana taimaka kwarai wajen kawo hadurra. Saboda da yawa yara basu san dokokin tuki ba, wasu kuma basu kai mizanin da za’a ce an fara basu motoci suna hawa ba.
The post Hatsari ya lalata Mota 6 a Abuja appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us