Likitocin Jihar Ekiti sun nemi Fayose ya biya su albashin su
– Likitocin Jihar Ekiti na shirin tafiya zanga-zanga domin Fayose ya biya su kudaden albashin su
– Likitocin na bin gwamnatin Jihar albashin watanni 4
– Majinyata sun fara komawa asibitin gwamnatin Tarayya
Gwamna Ayodel Fayose na jihar Ekiti na fuskantar matsi domin likitocin Jihar na shirin tafiya yajin aiki domin su nemi a biya su kudaden albashin su na watanni 4 wadanda ya rike bai biya su ba.
KU KARANTA: Mun karya alkadarin yan kungiyar Boko Haram – buhari
Dakta John Akinbote, shugaban rashin kungiyar Likitoci Ta kasa (NMA) ya bayyan cewa yajin aikin yayi daidai domin ma’aikata aikin lafiya ba’a kulawa dasu wanda hakan bai kamata ba.
Inda yake magantawa a Jaridar The Ounch, yace ” Ya kamata mutane su fito suyi magana a biya mu albashin mu. Watanni 4 ke nan ba’a biya mu ba.
” Kowa ya san ana wahalar mai. Ya’yan mu na zuwa makaranta kuma dole mu biya masu kudin makaranta. Da kuma sauran kudaden da zamu biya.
” Idan ba muyi yajin aiki ba gwamnati kawai share abun zatayi. Wannan ba fadan mu bane kawai ahr da na sauran ma’aikata. Fannin lafiya cigaba da lalacewa kawai yake yi sakamakon rashin biyan kudaden.
Ya kumayi kira ga gwamnatin jihar data yi wani abu tun kafin yajin aikin yayi tsanani sosai.
Rahotanni kuma sun nuna cewa yan uwan majinyata na neman a canza ma yan uwan su asibitoci inda suke komawa asibitocin gwamnatin tarayya.
Wani jami’i wanda baya so a bayyana sunan shi ya bayyana cewa yana sa ran cewa yajin aikin ba zaya dade ba sosai gwamnati zata baiya kudaden.
A wani labarin kuma, yan Najeriya sunyi Allah wadai da kiran da gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti yayi akan cewa kada China ta ba Najeriya aron kudade. Gwamna ya tafi kasar ta China kwana 2 bayan da shugaba Buhari ya tafi ziyarar kwanki 4. Ya rubuta wasika ga gwamnatin Jihar inda ya nemi kada a bada Najeriya bashin ko sisi. Wannan ya jawo mashi Allah wadai daga yan najeriya inda wasu suka nemi gwamnatin Najeriya ta ja mashi kunne.
The post Likitocin Jihar Ekiti sun nemi Fayose ya biya su albashin su appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us