Okorocha ya maganta akan ba Igbo takara da PDP tayi
– Rochas Okorocha ya bayyana cewa matakin da PDP ta dauka don ba Kudu maso Gabas takarar mataimakin shugaban kasa a takara 2019 abun dariya ne
– Ya bayyana cewa PDP bata taba sanin kudu maso Gabas nada amfani ba saida ta fadi takara
– Okorocha ya bayyana cewa PDP ta zagi kabilar Igbo
Gwamna Rochos Okorocha, gwamnan Jihar Imo, ya bayyana cewa takarar da jam’iyyar PDP ta ba kabilar Igbo muguwar kyauta ce irin ta mutanen Girka.
KU KARANTA: Shugaban hukumar NYSC ya maganta akan karin kudaden masu yima Kasa Hidima
Gwamna Okorocha ya bayyana hakan ne inda yake bayyana cewa jam’iyyar PDP ta zagi kabilar Igbo da wannan kyautar data yi masu. Jaridar The Nation ta ruwaito.
Gwamnan ya bayyana wannan ne ta hanyar Sam Onwuemeodo, babban sakataren shi, inda ya bayyana cewa sai yanzu PDP ta gane cewa kudu maso Gabas zata iya samun kujerar mataimakin shugaban kasa shekara 1 bayan data fadi zabe.
Yace ” Sai yanzu jam’iyyar PDP ta gane cewa kudu maso Gabas, a matsayin shi na yanki mai girma zaya iya samun kujerar mataimakin shugaban kasa shekara 1 bayan data fadi zabe. Sai yanzu suke farkawa daga gyangyadin da suke yi.
” PDP bata taba mari muka samu shugaban kasa ba, mataimakin shugaban kasa, shugaban majalisar dattawa ko kuma shugaban ,ajalisar wakilai. Kudu maso Gabas bai samu komai ba a shekaru 16 na mulkin jam’iyyar PDP a Najeriya.
” Abunda ke akwai shine, kudu maso Gabas zata samu nata kason a gwamnatin APC. PDP ta riga ta bata rawar ta. APC baza tayi haka ba.
A kwanakin baya ne jam’iyyar PDp ta bayyana cewa tana shirin ba kudu maso gabashin Najeriya takarar mataimakin shugaban kasa, mai bada shawarar shari’a da kuma mukamin shugaban matasa a 2019. Wannan yazo ne bayan da jam’iyyar ta yanke shawarar ba dan Arewa takarar a 2019.
The post Okorocha ya maganta akan ba Igbo takara da PDP tayi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us