Abunda yasa aka cire tallafin Mai a Najeriya
– Hukumar PPRA ta bayyana dalilan daya sanya aka cire tallafin Mai
– Ta bayyana cewa canjin kudi babban kalubale ne
Gwamnatin Najeriya ta bayyana dalilan daya sanya aka cire tallain Mai. Jaridar Premium Times ta bayyana cewa PPRA ta fadi cewa dama cire tallafin Man wani abu ne wanda ya kamata ace anyi.
Yan Najeriya da yawa sun nuna rashin gamsuwar su akan yadda Mai ya tashi inda daga Naira 86.5 yanzu zaya koma N145.
KU KARANTA: Tsagerun Nija Delta sunyi barana a kaina – Minista
Wannan ya jawo karuwar Mai izuwa kashi 67. Mr Iyonyo wanda shine mukaddashin Sakataren hukumar PPPRA ya bayyan a cewa anyi karin ne domin bawa masu shigo da Mai dama su samu canza mudaden su cikin sauki domin shigowa da wadataccen Mai ba tare da wani babban kalubale ba.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta maganta akan hakan inda tayi Allah wadai kuma ta bayyana cewa zata kalubalanci cire tallafin Man tare da sauran kungiyoyi.
” CIre tallafin Mai da gwamnati tayi abun Allah wadai ne kuma zamu kalubalanci hakan tare da sauran kungiyoyin sa kai gaba daya.
“Bayan tilasta karin kudin wutar lantarki da akayi, ga karfewar Naira ga kuma tashin kayan masarufi, daya daga cikin abubuwan da babu wanda za yayi tsammani shine cire tallafin Mai.
” Wanna karin kudin da akayi ba a taba irin shi ba a Najeriya inda ya zamu anyi kari da kashi 80. Bama hakan ba, an alakanta shi ta haramtacciyar hanya.
Yan Najeriya da yawa a shafukan sada zumunta suna magantawa inda kowa ke bayyana ra’ayin shi game da karin farashin Man da akayi.
The post Abunda yasa aka cire tallafin Mai a Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM (Nigerian newspapers).
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us