Al-Mustapha ya bayyana zahirin abunda ya kashe Abacha, Abiola
-Manjo Al-Mustapha wanda ya dauke matsayin mai ba tsohon shugaban soja, Janar Sani Abacha yace wanda Abacha bai saci kudin Nijeriya ba kamar yadda ya yadu
-Ya nace akan ya boye kudin ne a kasashen waje domin amfanin nan gaba
-Yake yi alkawarin bayyana sojojin dake bayan kisan Janar Abacha da Cif MKO Abiola
Mai girma Hamza Al-Mustapha wanda ya kasance tsohon shugaban masu tsaro ga margayi tsohon Janar Sani Abacha ya bayyana cewa yasan sojojin da ke da alhakin kisan tsohon shugaban shi.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Al-Mustapha inda yayi magana a jihar Lagas, a ranar Litinin, 30 ga watan Mayu, ya kuma cewa bai ji dadi ba kan daukar hoton da kafafen yada labarai suka yi kan kudin da Abacha ya ajiye a kasashen waje ba.
KU KARANTA KUMA: An aika dakarun sojoji da ta murkushe Niger Delta Avengers
Al-Mustapha yace a wani gamuwa a babban birnin tarayya wadda ya hada da shuwagaban gargajiya, jiga jigan yan siyasa da kuma wasu mambobi na kungiyar Abacha, an amince akan saboda kashedi daga kasashe daban daban, ya zama wajibi a tsaya akan ninkaya da boye wasu kudade a kasar waje.
Yace; “Janar Sani Abacha ya bauta wa kasar nan na tsawon shekara hudu da watanni, kuma a cikin wannan lokacin, ya taka mutane da yawa, idan aka ajiye juyin mulki da yayi sau biyu ko uku da jama’a suka sani, akwai wasu da dama da ba’a bayyana wa jama’a ba.
“wadannan masu hadin gwiwa da wasu mambobin kasashe daban daban sun lankwasa akan cire shi daga ofis. Janar Abacha ya zama mattace a yau amma wadannan sojoji basu yafe mai ba har yanzu. Lokacin da yake raye, makiyan Janar Abacha tare da al’umomin kasashe daban daban, sun kuma yi barazanar gabatar da mallaka akan kasar.
“Akwai wani zama a babban birnin tarayya Abuja, inda a ka amince akan ajiye kudade a kasan waje saboda idan lokacin mallakan ya zo, wannan kudin zai ci gaba da ninkaya Nijeriya. Tom Ikimi ya kasance sakataren harkokin kasashen waje a lokacin.
KU KARANTA KUMA: Ku karanta tarihin kasar Najeriya mai bayani
“ A wannan lokacin ana siyar da man petir akan dala bakwai ko takwas. Mun ci bashi domin gudanar da tattalin arziki kuma lokacin ne aka samar da kungiyar Petroleum Trust Fund (PTF). Na ji kunya yayinda nake gidan yari da naji abunda mutane suka kira da ‘satan kudin Abacha’. Nayi rubutu zuwa ga iyalan marigayi Abacha daga gidan yari, dasu bayyana wa jama’a ko wadannan kudin a sunan shi suke, kwanan watan kafin yay a zama shugaban kasa ko kuma bayan da ya zama shugaban kasa.
“Na kasance a gurin gamuwan da aka yanke shawaran amma saboda dukkanmu bamu samu barin gidan shugaban kasa ba, sai da na koma kafin lokacin gamuwan yakare. Kaman yadda na fada, Abacha ya taka mutane wanda har yanzu basu yafe mashi ba ko da ya mutu.
“Ka kuma tuna da cewa Abacha ba wai yana fita daga kasar bane. A farkon mulkinshi, ya je kasar Pakistan, Saudi Arabia da kuma wasu kasashe a cikin shakara ta 1994. Yawancin tafiyarshi cikin kasashen Afrika ne, toh tayaya zai iya sanya wadannan kudin a kasashen waje?
“A yayinda nake CSO din shi, bankin ajiya da nake dashi ya kasance tare da Bank of the North kuma anan ake biyan albashi na. Na tafi hukumar sojoji domin na bauta wa kasa ta ba wai domin nayi kudi ba tunda na fito daga gidan arziki.”
Al-Mustapha ya nemi yan Nijeriya da su lokaci ya gama da matsalarshi ta kotu kafin ya bayyana sojojin dake da alhakin kisan Abacha da kuma Moshood Abiola.
“Kamar yadda na fada a gaban Oputa Panel, abunda ya kasha Abacha shine ya kasha MKO Abiola. Ina dai rokon ka da kayi hakuri; da zaran na gaama da kotu, za’abbayyana su a jama’a zasu kasance a kundi uku.
Ya nace akan shi ba mamba na ko wani jam’iyya bane amma y ace Shugaba Muhammadu Buhari mai gaskiya ne wadda ke son Nijeriya.
“Janar Buhari dan Nijeriya ne mai gaskiya wadda aka ja cikin siyasa. Babu wanda zai iya jayyaya da son da yake yi wa kasar Nijeriya. Ko makiyansa zasu amince da haka. Kuma wadannan ne halayen da muka gani daga gare shi; da yasa muka amince dashi a matsayin shugaban Petroleum Trust Fund”
Ahalin da ake ciki, Al-Mustapha ya zargi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da bata suna ya kuma bukaci da ya kawo hujja akan amfani da maharbi 1000 domin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan gabannin zaben shekara ta 2015 a gurin mahawara.
The post Al-Mustapha ya bayyana zahirin abunda ya kashe Abacha, Abiola appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us