Abubuwa 10 game da wanda zai yi gaji Adams Oshiomhole
– Yaki ya fara a tsakanin jam’iyyar People Democratic Party (PDP) da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin zaben gwamna da zai za a yan watanni masu zuwa
-Godwin Obaseki ,ya fito a matsayin dan takaran jam’iyyar APC, a ranar Lahadi, 19 ga watan Yuni, yayin da aka ayyana Osagie Ize-Iyamu, a matsayin wanda ya lashe zaben zango na farko , a jam’iyyar PDP,a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni
-Obaseki da Ize-Iyamu ne manyan yan takara, wanda zasu kara neman zaben gwamna a jihar Edo, a watan Satamba, a matsayin wanda zaiyi nasara kan gwamna Adams Oshiomhole
Wadanda suke Ja gaba, a cikin wannan zaben gwamna, na jihar Edo da ke zuwa, sun kasance sananun makiya. Dukansu sun kasance a cikin sansanin siyasa daya, kafin bambance-bambance siyasa ya sa su raba hanya.
Obaseki, zai fito dan takaran jam’iyyar APC, Osagie Ize-Iyamu wanda ya fito a ranar Litinin, 20 ga watan Yuni a matsayin mai takara a jam’iyyar PDP zai yi takara da shi.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya bayyana a ofishin sa cikin koshin lafiya bayan ya dawo daga ganin likita
1. An haifi Ize-Iyamu a jihar Edo, a ranar 21 ga watan Yuni, 1962. Ya fito daga karamar hukumar, Iguododo, Orhionmwon, na jihar Edo.
2. yayi karatun firamari a St.Joseph primary school da Ebenezer Nursery and primary school a birnin Benin. Yayi makarantar gaba da firamari a Edo college of premier secondary school a jihar Edo. Daga nan ya je jami’ar University of Benin in da ya karanci fannin shari’a
3. Osagie Ize-Iyamu dan siyasa ne a Najeriya kuma Pasto a Redeemed Christian Church of God (RCCG) kuma tsohon shugaban ma’aikata kuma sakatare ga gwamnatin jihar Edo.
4. Ya kasance babban mamba a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin ya koma jam’iyar People Democratic Party (PDP).
5. Ize-Iyamu, ya kasance mataimakin chiyaman na kasa a defunct Action Congress, yankin kudu masu kudu.
6. Ya kasance darakta janar a kungiyar tsara yakin neman zabe ga Adams Oshiomhole, amma sun rabu da gwamnan daga baya.
7. Ya lura da ofishin yakin neman zaben Goodluck/Sambo, suma ya ba da nashi gudunmawar ga kungiyar.
8. Ya kasance chiyaman na karamar hukumar Oredo, birnin Benin, a shekara ta 1983.
9. Ya baje kolin ilmin sa a gudanar da harkokin kasuwanci a lõkacin da ya kafa I.O Farms Training Institute, wanda yake a al’umma Ugbor-Amagba, babban birnin Benin,jihar Edo.
10. Ya samu girmamawa kwanan nan a Benson Idahosa University, makarantar kudi na Higher Istitution of Learning a jihar Edo.
The post Abubuwa 10 game da wanda zai yi gaji Adams Oshiomhole appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us