DSS sun kama shugaban kwamitin Buhari kan zamba
-An kama wani mamba na kwamitin binciken makamai
-An kama Air Commodore Umar Muhammed (mai ritaya), kan zargin zamba tare da manyan jami’an gwamnati
-A halin yanzu, Muhammed na tsare a hannun hukumar Department of State Security (DSS)
Hukumar Department of State Security (DSS) sun kama wani mamba a kwamitin masu bincike a kan samuwar makamai na kasa. An kama mamba, Air Commodore Umar Muhammed (mai ritaya), kan zargin aikata zamba tare da wasu manyan jami’an gwamnati.
Wata majiya ta bayyana wa jaridar Thisday cewan, ana zargin Muhammed da jagorar wasu manyan jami’ai cikin hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) da kuma hukumomin tsaro gurin aikata mugayen ayyuka.
KU KARANTA KUMA: Kungiyar CPPM sun bukaci Buhari da yayi bincike
An ce Muhammed ya kasance chiyaman na EasyJets Nigeria, kuma daya daga cikin mambobi 13 dake bincike a kan makamai,wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya a watan Augusta na shekarar da ta wuce karkashin jagorancin kungiyar Office of the National Security Adviser (ONSA).
A halin yanzu, hukumar DSS ta bayyana cewa shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), Ibrahim El-Zakzaky na tsare da kan sa.
The post DSS sun kama shugaban kwamitin Buhari kan zamba appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us