Sports Betting

Trending

random

Abun da Saraki da Ekweremadu zasu fuskanta a Kotu

–  Da alamun Shugaban Majalisa Dattawa, Bukola Saraki, da mataimakin sa , Senata Ike Ekweremadu,zasu fuskanci beli mai tsanani idan aka gurfanar da su a kotu ranar litinin, 27 ga watan yuni.

–  Wata majiya a majalisar tarayya ta bada labarin cewa ma’aikatar shari’ar tarayya na shirin tilasta ma alkalin babban kotun Abuja, Jastis Yusuf Halilu, da ya tsananta beli akan wadanda ake tuhuma.

–  Ana tuhumar Saraki,  Ekweremadu, da wasu 2 akan laifin yin aikin yan jabu na dokokin majalisa tarayya.

–   Shugaban majalisar da mataimakin sa , Ike Ekweremadu kan shiga mawuyacin halin idan tuhumar da ake musu gaskiya ne.

Saraki-Ekweremadu

Saraki-Ekweremadu

Za’a gurfanar da Shugaban majalisa dattawa, Mataimakin da da wasu guda biyu a kotu , akan yin aikin yan jabu da cuta.

Bugu da kari, Shugaban majalisan da mataimakin sa zasu fuskanci tsanani a kotun, a sakamakon labarin da wata majiya daga cikin majalisar ta fada, ta bayyana cewa ma’aikatar shari’ar tarayya na shirin tilasta wa alkalin kotun, Jastis Yusuf Halilu, ya ba su matsananciyar beli.

“Kaidin da ake shiryawa shine, a basu beli mai tsananin da ba za su iya cikawa da wuri ba. Belin irin wanda zai sa su dade a kotun ne kafin su iya fita. Majiyar ta fada ma Jaridar This Day

Ya ce: “Wannan shari’ar akwai siyasa a cikin ta kuma ma’aikatar shari’ar baza ta bari su fita da sauki ba. Sai sun sha bakin wahala da dogon lokaci kafin su iya fita daga cikin kotun.”

Amma, gwamnatin tarayya ta yiwa Saraki da Ekweremadu alkawarin adalci a shari’ar idan suka gurfana a kotu. Gwamnatin ta fadi hakan ne ta ministan shari’a kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, a ranar Alhamis , 23 ga watan yuni.

KU KARANTA: Ba mu muka canza dokokin zaman majalisa ba-Mai Kasuwa

Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa Ministan shari’an nanata cewa sai shugaban majalisa da mataimakin sai sun gurfana amma za ayi musu rahusa. A wani jawabi da ya bayar ta mai magana da yawun sa, Mr Salihu Othman Isah, Abin takaici ne majalisa dattawa ta tuhume mu da cin fuskar bangaren dokokin kasa ta shirin tsige Shugabannin ta.

The post Abun da Saraki da Ekweremadu zasu fuskanta a Kotu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Abun da Saraki da Ekweremadu zasu fuskanta a Kotu Reviewed by Olusola Bodunde on 08:58 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.