Sports Betting

Trending

random

Ramadan: Abubuwa 5 da ya kamata magidanta su kiyaye

Watan Ramadan wata ne da ya kamata magidanta su kyautatawa iyalansu; wadannan shawarawari su za su taimaka wajen ganin an yi hakan:

KU KARANTA: Dokar Hana Addini ta Sabawa kundin tsarin mulki – Osinbajo

all fathers

Wani magidanci na cin abinci da iyalinsa a yayin buda baki ko sahur

  1. Cin abincin tare da iyali

Cin abinci da jama’a na sa kauna da son juna. Ballantana a tsakanin iyali, yana da kyau magadanta su rika yin sahur da buda baki tare matansu da ‘ya yansu a wuri guda.

  1. Karantun Qur’ani tare

Karatun al Qur’ani a watan Ramadan na da falala mai yawa, don aka yana da kyau magidanta su rinka karatun Qur’anin da iyalan su domin samun albarka da kuma lada mai yawa.

  1. Umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna

Ramadan wata ne da ake nunka ladan musulmi idan ya yi aikin alheri, haka ma idan ya aikata ba daidai ba. Yana da kyau mu hori iyalan mu da aikata kyakkyawa tare da hana su aikata mummuna a wannan watan.

  1. Karfafar yara da su jurewa azumi

Yana da kyau a karafawa yara da shekarunsu ya kai (10 zuwa 14), da su yi azumi. Idan sun dauka kuma a karfafa musu gwiwa a ga sun kai. Komai wahala in har sun dauka to kar a bari su karya. Yana da kyau a yaba musu in sun kai azumin. Haka zai sa su saba kafin su balaga.

  1. Kyautatawa Iyali: Sayawa yara abubuwan da za su faranta musu

Ramadan wata ne na kyautatawa da farantawa juna. Yana da kyau magidanta su kyautatawa matan su ta hanyar da duk ta dace. Yara ma haka.

 

The post Ramadan: Abubuwa 5 da ya kamata magidanta su kiyaye appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Ramadan: Abubuwa 5 da ya kamata magidanta su kiyaye Reviewed by Olusola Bodunde on 08:58 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.