Sports Betting

Trending

random

A’isha Buhari ta ba Fayose kwana 5 ya janye zargin kanta

Uwar gidan shugaba Buhari, A’isha Buhari ta rubuta takarda zuwa ga gwamnan Ekiti Ayo Fayose tana bukatar ya janye zargin sa a kan ta. Shi dai gwamnan kwananan ne ya zargi uwar gidan da cewar tana da hannu cikin badakalar kudin Halliburton.

gwamna fayo kenan

Uwar gida A’isha ta rubuta tare da aika takardat zuwa ga gwamnan ta hannun wakilan ta lawyoyi. A cikin takardar ta bayyana cewa gwamnan shine ummul haba’isin yada zargin da ake yi a kanta a kafofin yada labarai.

Kafar yada labarai ta Premium Times ce dai ta samu takardar da aka aikewa gwamnan ta kafar aike-aike jiya laraba 22 ga watan nan. Takardar dai kamar yadda gidan Jaridar ya samo tana dauke ne da cewar Uwar gidan ta Shugaba Buhari tana bukatar gwamna Fayose da ya janye maganar tasa cikin kwanaki biyar domin a cewar su maganar bata da tushe balle makama ko kuma ya fuskanci sammaci a kotu.

Ku karanta: Ban da Matsala da Ali modu sheriff -Makarfi

Shi dai gwamna Fayose ta hannun wasu mukarrabansa a kwanan baya yace A’isha Buhari tana da hannu dumu-dumu cikin badakalar Haliburton inda aka ce ta karkatar da $170,000. Daga baya kuma A’isha Buhari ta kafar sadarwar zamani na tuwita ta yi wasu kalamai da gwamnan inda ta kirashi “kare maras linzami”. A wani labarin kuma hukumar EFCC ta daskarar da asusun gwamna Fayose saboda zargin kudin makamai da ke ciki.

The post A’isha Buhari ta ba Fayose kwana 5 ya janye zargin kanta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


A’isha Buhari ta ba Fayose kwana 5 ya janye zargin kanta Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.