Sports Betting

Trending

random

Akinwumi Adesina yaci lambar yabo ta FARA

-Tsohon ministan gona Akinwumi Adesina ya ci lambar yabo ta FARA na shugabanci a Africa

-Adesina, ya amshi kyautar ne a Kigali Baban birnin Kasar Rwanda

-Ya ayyana amsar kyautar ga manoman Africa

-Adesina yace lallai Nigeria ta bada kokari wajen ciyar da kanta

Tsohon Minista

Wani tsohon Minista a karkashin Jonathan da kuma shugaban Banki na Cigaban Nahiyar Afirika mai suna Dakta Akinwunmi Adesina

Kungiyar masu binciken hanyoyin noma a Africa wadda ake kira da turanci FARA a takaice ta bashi lambar yabo wajen shugabanci da nuna fasaha ranar Litinin 13 Yuni, 2013.
Adesina Wanda shine shugaban bankin raya Africa (AfDB) yayin da yake amsar kyautar a bikin fasahar noma na sati guda da akayi Na bakwai, ya danganta kyautar da manoman Africa.
Shugaban gwamnatin Rwanda Mr. Anastase Murekezi ya mika kyautar ga Adesina.

A jawabinsa Mr. Murekezi yace “ba zamu cima gurinmu ba a aikin noma sai munyi amfani da ilmin kimiyya da fasaha” Ya cigaba da cewa “ba wai kawai mu rika shigowa da fasahar noma daga wajeba, ya zama wajibi mu kirkiro namu wadanda suka dace da yanayinmu, haka kuma ya kasance bincike-binciken suna da tasiri ga manoma.

A bayanin Adesina kafin ya karbi kyautar, yace dole ne Nigeria ta ciyar da kanta ta amfani da dimbin matasa da take da su ta hanyar noma. Shi dai Mr. Adesina, masanin tattalin arziki ne wanda ya shafe shekaru 25 yana aiki da hukumomin kasa da kasa a kan ayyukan gina kasa. Haka kuma yayi karatu daga digiri na farko har digirin digirgir a jami’oi da yawa.

Yanzu shine shugaban bankin raya Africa (AfDB) Na takwas. Kafin nadinsa ya rike mukamin ministan gona tsakanin shekara 2011-2015 a gwamnatin Nigeria. A cikin ayyukan da yayi sun hada da shekara goma da yayi a cibiyar Rockefeller inda ya rike mukamin mukaddashin darakta a garin New York.

The post Akinwumi Adesina yaci lambar yabo ta FARA appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Akinwumi Adesina yaci lambar yabo ta FARA Reviewed by Olusola Bodunde on 05:03 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.