Sports Betting

Trending

random

Chile ta buge Colombia zuwa wasan Karshe a gasa

– Chile ta ba Colombia kashi, ta kai zagayen karshe na gasar Copa American Shekarar 2016.

 – ‘Yan wasa; Charles Aranguiz da Jose Fuenzalida suka ci ma Kasar Chile kwallayen.

– Kasashen biyu sun tabawa karara a wasan zagayen karshen gasar shekarar 2015, inda Chile tayi nasara.

Chile

 

 

 

 

 

Kasar Chile ta buge Kasar Colombia da ci 2 da nema, wannan na nufin za ta hadu da Kasar Argentina ta su Lionel Messi a wasan Karshe. Ana take wasa Charles Aranguiz da kuma Jose Fuenzalida suka zura kwallo a ragar Colombia, wannan dai zai zama Kasar Chile masu lakabin ‘La Roja’ sun kai zagayen karshe sau 2 kenan a jere duk da cewa ba su da wani uban ‘yan wasa a kasa. Kwallayen dai sun kai Kasar Chilen wanda ta rasa ‘yan kwallon ta, zuwa wasan karshe, inda za ta kara da kasar Argentina a gasar ta zakarun nahiyar Amurka na wannan shekara ta 2016.

Duk da cewa Kasar Colombia ta kai hare-hare da dama, amma bata samu leka ragar Chile ba a wasan. Kasar Chile dai ta lallasa Kasar Mexico da ci 7 da nema, wasan da Arturo Vidal ya samu kati, wanda ya sa bai buga wasan Colombia ba. Haka kuma wanda ke buga tsakiyar tare da Arturo Vidal wani Marcelo Diaz shi ma ya samu rauni a katare wanda hakan ya hana sa buga wasan shima. Amma duk wannan bai hana yaran Koci Juan Antonio Pizzi yin nasara ba.

Wasan karshen da za a kara tsakanin Argentina da Chile zai zama mai-man wasan karshen gasar shekarar 2015 inda Kasar Chile tayi nasara, Alexis Sanchez shi ya ci ma Kasar sa kwallon a wannan lokaci. Su kuwa Argentina sun ba Kasar Amurka dan Karen kasha ne, da ci 4-0. Masu harsashe da kwararru dai a harkar Kwallon kafar suna ganin Argentina za tayi nasara wannan karan. Bari ma, tun a wasan su na farko a gasar shekaran nan, Argentina ta buge Chile da ci 2-1.

Leo copa

 

 

 

 

Yanzu dai idon duniya na kan Kasar Argentina, wanda rabon kasar da daga wani babban kofi kuwa tun shekarar 1993, da ta ci gasar Copa American.

The post Chile ta buge Colombia zuwa wasan Karshe a gasa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Chile ta buge Colombia zuwa wasan Karshe a gasa Reviewed by Olusola Bodunde on 08:01 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.