Gwamnati ta fara gyara lalatan da Tsagerun NDA sukayi
– Gwamnatin tarayya ta fara gyaran kafufuwan man da tsagerun neja delta suka lalata
– Sojoji sun raka masu gyaran wurin domin tabbatar da tsaro
– Wannan na faruwa ne bayan tsagerun neja delta sun ce kada gwamnati ta gyara.
Gwamnatin tarayya tayi kunnen kashi ta fara gyaran kafufuwan man feturin da Tsagerun Neja Delta suka lalata.Tsagerun Neja Deltan sun dauki alhakin lalata kafufuwan kamfanonin sarrafa man fetur a yankin ta Neja Delta, kuma tayi gargadin cewa kada fa gwamnati ta sake ta gyara . Kungiyar yan bindigan ta yi gargadi a ranar 13 ga watan yuni cewan kada fa gyara duk bututun da ta sanya wa bam har sai idan anyi sulhu.
“ Zamu cigaba da lalata kafufuwan idan gwamnati da kamfanonin mai basu bi umurnin mu ba na kada su yi gyara, har sai idan an samu sulhu.”
Yan bindigan sun sanya wa bututun kamfanin gas a ranar 26 ga watan Mayu a Ubefan Gbaramatu ta karamar hukumar Warri kudu maso yamman Jihar Delta. Amma duk da gargadin su, Gwamnati ta fara gyara a yankin.
Jaridar vanguard ta bada rahoton cewa rundunar sojoji suna nan tsare da masu gyaran . Mazauna unguwannin sun tabbatar da cewa Sojoji na raka su da jiragen ruwa cike da kayan gyara zuwa wuraren da aka lallata.
KU KARANTA: rabuwar kai tsakanin yan bindigan neja delta
Chif moses bebeninibo wanda shine Shugaban unguwannin kunukunuma ya tabbatar da cewan gyara na gudana amma kamfanin da ke gyaran ‘melcurt Nigeria limited’ basu dau yan yankin a matsayin ma’aikata ba. Yace ko tayi ba’ayi wa yan yankin ba, kuma sina tuhumtar gwamnatin tarayya da kawai ta damu da man fetur din su ne , bata damu da su ba.“Abin da suka iya shine tsorata damu da Sojoji Amma ba du damu da koshin lafiyan mu ba”.
The post Gwamnati ta fara gyara lalatan da Tsagerun NDA sukayi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us