Sports Betting

Trending

random

Hukumar Efcc ta kasa zata gurfanarda Warifa Dudafa

-Hukumar Efcc ta kasa zata gurfanarda Warifa Dudafa tsohon babban mai ba tsohon shugaban kasa shawara Goodluck jonathan na harkokin sha’anin cikin gida akan zargin da ake mai na handame kudi har kimanin N1.6bn.                                                

– Ankama Dudafa akan zargin da ake mai na raba har zunzurutun kudi kimanin N10bn ga masu zaben fidda gwani na shugaban kasa a shekara ta 2014.                                                  

 -Za’a tuhumeshi ne tare da Iwe Nna wanda aka fi sani da Taiwo Ebeneza da Olugbenga Isiah.    

Jonathan's cousin

Goodluck Jonathan

Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa (EFFC) zata gurfanar da babban mai ba tsohon shugaban kasa  Goodluck jonathan shawara kan sha’anin cikin gida Waripamowei Dudafa akan zargin da ake mai na cinye kudi har N1.6bn.Kunji cewa (EFFC) ta taba cafke Dudafa a filin saukar jirgin sama dake jahar lagos kan raba kimanin kudi N10bn ga masu zaben fidda gwani na shugaban kasa a shekara ta 2014.Daga rohoton da muka samu na jarida Punch munji cewa za’a tuhumi Dudafa ne tare da wani Iwe Nna wanda ake kira wasu lokutta Taiwo Ebeneza da Obgbenga Isiah.

Zasu bayyana a gaban mai shari’a Muhammad Idris a babbar kotu da ke Abuja babban birnin tarayya.  Alkalin ya bayyana cajin farko ga wanda ake tuhuma ranar ko kafin 11 ga watan Yunin 2013,a garin Lagos “Inda za’a cigaba da sauraren kara akan zarginsu da akeyi na hadame kudaden har N1.667bn.

Laifin ya saba ma tsarin dokar kasa shafi na 18(a)na haramta hamdamar kudi da da hukunci  na tsarin dokar ta 17(a)na kudin tsarin mulki na shekara ta 2012.Sauran abubuwan da ake tuhumar Dudafa da su sun hada da kamfanoni guda 6 da yake dasu;Seagate proporty Development and Investment Limited,Avalon Global property Development Company Limited,Ebiweise Resources pluto Property and Investment company,Rotato Interlink service and Dejakes Fast Food Restaurant Nigeria,wanda ya boye adadin yawan kudin tskanin wata Yuni na 2013 zuwa Afrilu 2016.Hukumar (Efcc) tana da shaidu 21 wanda ya hada da wakilan bankuna dan tabbabtar da gaskiya akan wanda ake tuhuma.

The post Hukumar Efcc ta kasa zata gurfanarda Warifa Dudafa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Hukumar Efcc ta kasa zata gurfanarda Warifa Dudafa Reviewed by Olusola Bodunde on 05:03 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.