Sabuwar APC Ta Kunno Kai A Jihar Kaduna
Kamar yadda majiyar mu ta Dailytrust ta ruwaito cewar wata sabuwar APC ta kunno kai a jihar Kaduna mai suna ‘APC Akida’ wanda kuma.
Tom Maiyashi ne ya zama shugabanta sai kuma Alhaji Ibrahim Yaro ya zamo mataimakin sa sannan kuma Hafsat M. Baba itace ta zama magatakardar sabuwar jama’iyyar watau sakatariyya. Wadannan sabbin shuwagabannin kuma har ilayau sun bayyana cewa zasu bayyana sauran jigogin jam’iyyar tasu na kowane mataki a nan gaba kadan.
Maiyashi kuma ya kara da cewa APC Akida zata samar da wani yanayi ne da duk yan APC din masu akida zasu fito domin su bada gudummuwar su a cigaban jihar. Wasu daga cikin jigogin sabuwar jam’iyyar dai a wajen taron bada mukaman sun hada da Sanata Shehu Sani da kuma Hakeem Baba-Ahmed.
Mahalarta taron kuma sun bayyana cewa kafa sabuwar Jam’iyyar ya zama wajibi ne saboda yadda wasu yan tsiraru suke juya babbar jam’iyyar a jihar ba tare da sanin ya kamata ba. Sannan kuma suka bayyana cewar a makonni masu zuwa kuma jam’iyyar tasu zata dukufa sosai wajen samun mabiya a duk fadin jihar.
A cewar shugaban jam’iyyar “mu mun yadda da yin siyasa ba da gaba ba”. Ya kuma kara da cewa “mu mun kafa wannan jam’iyyar ne domin ganin yadda uwar jam’iyyar tamu tayi watsi da bukatun mu da kuma kaucewa tsarin da aka kafa jam’iyyar a bisa, kuma daya daga cikin manufofin mu yanzu shine ganin yadda zamu gyara jam’iyyar a kowane mataki”.
Sannan kuma shugaban ya yi kira ga Gwamna El-rufa’I da kara maida hankali wajen yima jama’a aikin da suka zabe shi yayi.
Bayyanar wannan bangare dai yayi kama da yadda wani ban gare ya bayyana na PDP kafin zaben 2015 wanna a bisani wasu daga cikin yan ban garen suka fice suka koma APC.
The post Sabuwar APC Ta Kunno Kai A Jihar Kaduna appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us