Yadda EFCC ke tsare wadanda ake zargi bai dace ba?
Shugaban hukumar hana yima kasa zambar tattalin arziki (EFCC) Ibrahim Magu yace duk Wanda hukumar ta kama kuma ta tuhumceshi to yana da laifin zamba.
Shaihin malami Paul Idornigie ya ce wannan kalami bai kamata ba daga mutum mai kima kamarsa. Ya tunarsar da shugaban cewa a idon shari’a duk wanda ake zargi baya da laifi sai doka ta tabbatar.
KU KARANTA: Kungiyar Amnesty international tayi Allah wadai da Shell saboda Ogoni
Wannan kalami da Ibrahim Magu yayi ya jawo masa suka. Lokacin da Magu yayi hira a tashar Channels ya ayyana cewa hukumarsa na kiran masu laifi ne kawai.
Ya kara da cewa basu bin wadanda basu da laifi, kuma Suna bincike ta yadda aka Saci kudin Kafin su kama kowa.
A wani labarin kuma, fadar shugaban kasa ta bayyan cewa daga hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari zuwa yanzu, Najeriya tayi nasarar amso kudade masu yawa. An karbo Naira Biliyan 78, Dala Miliyan 9 da kuma kudi a Fan na Ingila da kuma Euro.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin tabbatar da cewa an amso duka kudaden Najeriya da aka sace domin ganin cewa an yima yan kasa hidima dasu kuma an tallafawa tattalin arzikin Tarayyar Najeriya domin rayuwar talakan kasar ta gyaru.
The post Yadda EFCC ke tsare wadanda ake zargi bai dace ba? appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us