Sports Betting

Trending

random

Yan Najeriya Zasu Roki APC Ta Cigaba Da Mulki – Minista

Yarima Tony Momoh wanda kuma tsohon Ministan Yada labarai ne yace yan Najeriya zaku roki shugaba Buhari yacigaba da mulki idan 2019 tazo saboda dadin da zasu ji cikin shekara biyu masu zuwa.

Tony-Momoh

A cewar shi “a hakikanin gaskiya a 2019 yan Najeriyar zasu rika rokon mu ne saboda kafin lokacin mutane dubbai ne zamu taimaka da ayyukan yi da kuma sana’o’I.” To a ganin ku wadannan da muka taimaka din baza su so mu cigaba ba”?

KU KARANTA: Dani Alves yayi wata wasika mai sosa rai zuwa ga Barcelona

Sannan kuma ya cigaba da cewa ” shiyasa nace zamu samu wasu nasarori masu yawa amma kafin nan fa sai anyi hakuri saboda gyara na da wahala. Amma a cikin shekaru biyu masu zuwa yan Najeriya zasu fara jin dadin mulikin Buhari”

Prince Tony Momoh dai shine shugaban jam’iyyar CPC na farko wanda akayi bayan da aka gama rigimar Sanata Rufai Hanga. Bayan da akayi hadin gwiwoyin jam’iyyu guda 3 a shi ba’a bashi wani baban mukami ba. Wanda hakan ya sanya aka daina jin duriyar shi kwanaki biyun nan.

Zaku iya karanta cikakkiyar hirar da akayi da shi a jaridar The Sun.

The post Yan Najeriya Zasu Roki APC Ta Cigaba Da Mulki – Minista appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.


Yan Najeriya Zasu Roki APC Ta Cigaba Da Mulki – Minista Reviewed by Olusola Bodunde on 03:18 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.