Sports Betting

Trending

random

An kammal cinikin Martin Skrtel zuwa Fernerbache

An kammala cinikin mai tsaron gidan kungiyar Liverpool Martin Skrtel don sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Fernerbache biyo bayan sahhale masa da Liverpool din tayi bayan shekaru takwasa da ya share yana buga mata wasa.

 

vllkyt2bt23kvlgl9g.83824981

an ruwaito cewa kocin Liverpool Jurgen klopp yana ganin ba sa bukatan Skrtel din.

 

Skrtel dan shekaru 31 ya dira a birnin Istanbul ne a ranan talata 12 ga want yulio inda kuma aka duba koshin lafiyarsa kafin cinikin nasa ya kammala da ya kai pam miliyan 5.5. sa’annan ya amince da albashin da zasu bashi. Ana zargin Skrtel ya bar Liverpool ne saboda da wuya ya rika samu hurumin fara wasa a kakar wasa mai zuwa koda yaushe ba kamar da ba.

Skrtel bayan rattafa hannu a Fernerbache

Skrtel bayan rattafa hannu a Fernerbache

Liverpool ta samu Karin gwarazan masu tsaren gida tun bayan siyo Joel Matip da suka yi da kuma jiran kammal cinikin Joe Gomez. Wanda hakan ke alamta cewa Klo zai kyale Skrtel ta tafi. Ruwa yayi tsami tsakanin Klopp da Skrtel ne dai tun a bara inda wasanni 27 kacal Skrtel ya buga a cikin wasanni 63 da kungiyar ta fafata a ciki, wanda shine karancin wasa da ya taba bugawa tun zuwansa kungiyara shekarar 2008.

 

Sai dai kuma Klopp ya fada ma Mario Balotelli cewa dole ne ya bar kungiyar Liverpool indai yana son cigaba a kwallo. Klopp ya kara da cewa akwai wasu kungiyoyin kwallo wadanda suke bukatan dan wasan, amma yana fatan zai dage ya cigaba da buga wasa yadda ya saba a baya. Kwallo daya kawai Balotelli dan shekaru 25 ya jefa a AC Milan inda aka bada aronsa, duk da cewa dai yayi fama da raunuka har na tsawo wata 3, Klopp bai bukatansa a Liverpool. Sai dai yace zai tamakaeshi ya dawo da iya kwallonsa kafin sallaman shi.

The post An kammal cinikin Martin Skrtel zuwa Fernerbache appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


An kammal cinikin Martin Skrtel zuwa Fernerbache Reviewed by Olusola Bodunde on 05:59 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.