Sports Betting

Trending

random

Kace-nacen tsige Buhari a shafukan jaridu

Najeriya ta dauki dumi a ‘yan kawankin nan dangane da rade-radin da ake yi na cewa majalisar dattijai na shirin tsige Shugaba Muhammadu Buhari, majalisar dattawan ta karyata rade-radin a shafukan jaridun kasar.

 

Majalisa

Majalisar Kasa

Jaridar Vanguard ta ranar Juma’a 13 ga watan Yuli, ta ba da labarin cewa, rade-radin cewa majalisar ta soma shirye-shiryen tsige shugaba Muhammadu Buhari, labarin kanzon kurege ne. Duk da cewa majalisar ta magantu kan lamarin da aka ce an kitsa shi ne a wani zama na sirri da majalisar ta yi, aka kuma tsiguntawa manema labarai abinda ya faru.

KU KARANTA: Buhari a kayan soji ya janyo kace-na-ce (Hotuna)

Kan wannan batu, Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ba za ta tofa bakinta kan lamarin ba, saboda abin da ya shafi majalisar ne. Sanarwar hakan ya fito ne daga bakin Ahmed Makarfi a ranar Alhamis 14 ga watan Yuli.

Ita ma jamiyyar UPP a wata sanarwa da ta fitar, kuma sakatarenta Sanata Aliyu Sahabi Abdullahi ya sa hannu, ta kwatanta yunkurin majalisar da cewa shaidanci da kuma sonm mayar da hannu agogon dimukuradiyyya a kasar baya.

KU KARANTA: Dogara ya koka da rashin shugabanci nagari

Wannan rade-radin aniyar majalisar ya janyo Allah wadai daga daidaikun jama’a da kuma kungiyoyi musamman a shafukan sada zumunta da tafka muhawara na internet, ko a taron ta na baya-bayan nan kungiyar ‘yan kabilar Ibo zalla ta Ohanaeze Ndigbo ta soki aniyar majalisar.

Rahotannina cewa shugaba Buhari ya mayar da martani ga aniyar majalisar a inda ya ce majalisar su tanadi kalaman da za su fadawa ‘yan Najeriya a matsayuin hujja.

The post Kace-nacen tsige Buhari a shafukan jaridu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Kace-nacen tsige Buhari a shafukan jaridu Reviewed by Olusola Bodunde on 05:59 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.