Sports Betting

Trending

random

Buhari ya buga sunayen barayin kasa – Aborishade

-Femi Aborishade ya zargi shugaban kasa Buhari da kasa cika alkawarin da yayi saboda yana cikin matsi

-Ya ce babu shari’a da ta bayar da kariya ga ambaton sunayen wadanda suka saci duykiyar kasa

-Ya ce baza’ayi la’akari da buga sunayen a matsayin zagi ba

Femi Aborisade yayi kira kan yiwuwar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na sumun matsa lamba daga wadanda suka saci dukiyar kasa, sakamakon kin buga sunayen wadanda suka dawo da kudade.

Dukiyar kasa

Femi Aborishade

Ma’aikatar bayani ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun dawo da kudi kimanin naira triliyan daya. Duk da haka, ya sama wa alkawarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba’a bayyana sunayen wadanda suka saci dukiyar kasar ba.

KU KARANTA KUMA: Dasuki ya zargi Jonathan kan dala biliyan 15 na makamai

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, masu yakin kare hakkin dan adam, sun ce dole ne shugaban kasa ya cika alkawarin sa kuma ya saki sunayen wadanda suka sace dukiyar kasa.

 “A ranar 4 ga watan Yuni na shekara 2016, gwamnatin tarayya ta buga makudan kudaden da aka dawo da su daga cikin dukiyar kasa da aka sace, kama daga kudaden cikin gida da na waje, da kuma lissafin abubuwa 239 wanda ya hada da gonannaki, filaye, ababen hawa, gidaje wadanda aka gama, da wadanda ba’a gama ba, daga 29 ga watan Mayu na shekara 2015 zuwa 25 ga watan Mayu na shekara 2016.

 “Duk da haka, ba’a bayyana sunayen wadanda suka dawo da abuwawan ba, kamar yadda gwamnati tayi alkawari cewa zata bayyana sunayen wadanda suka sace dukiyar kasar.”

 

The post Buhari ya buga sunayen barayin kasa – Aborishade appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Buhari ya buga sunayen barayin kasa – Aborishade Reviewed by Olusola Bodunde on 03:59 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.