Gwamma Buhari da Jonathan – Dattawan Neja Delta
– Dattawan Neja delta sun tuhumci ‘yan bindigan yankin da yakin son kai ba don manufar yankin ba
– Suna yabawa shugaba Buhari na samun nasarorin sa
– Suna kira ga ‘yan Najeriya su goya ma Shugaba Buhari baya domin cika alkawuran da yama yan Najeriya
Dattawan yankin Neja Delta sun nuna goyon bayan su ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari saboda abubuwan da yayi a shekara daya, jonathan bai yiba a shekaraun sa. Yankin na fuskantar cigaban lalatan kafufuwan mai da yan bindiga keyi,musamman kungiyar tsagerun Neja Delta da suka sha alwashin cigaba da kai hare haren sai sun kwantar da sarrafa man Najeriya a yankin.
Jaridar Vanguard ta bada rahoton cewa wata kungiya mai suna ‘Concerned Niger Delta Elders (CNDE) ta tuhumci yan bindigan da yin ta’addanci don son ransu ,ba manufar mutanen yankin ba.
Shugaban kungiyar, Chif Ekayama Loyibo, yace wadanda ke adawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari sun manta cewa shine kwammanda in chif kuma zaben shi a kayi. Loyibo,wanda shine Arepamowei of Kabowei Kingdom kuma shugaban shugabannin Najeriya na samo zaman lafiya, yace shugaba Buhari ya musu a shekara daya abinda abinda Jonathan wanda yake dan yankin bai musu a shekaru 8 ba.
“Matsayar mu shine Buhari na nufin alheri ga yankin Neja Delta nuni da abubuwan da ya fara. Kuma ya kamata mu goya masa domin cimma manufarsa ga yankin. Idan kuka hada abinda Buhari yayi ma Neja Delta da abinda yaron mu kuma dan uwanmu ,Goodluck Jonathan,yayi a shekaru 6 da rabi, zaku yarda dani cewa Buhari yafi alheri a shekara 1. Saboda haka,mu goya wa Shugaban kasa da gwamnatinsa baya saboda ya canja mana yankin mu ta zama irin Legas da Abuja domin laifuffuka su ragu.”
KU KARANTA : Dasuki ya zargi Jonathan kan dala biliyan 15 na makamai
Baya ga wata, Shugaban cocin Victory Assembly, Bishap Jonathan Eze yayi gargadi ga tsagerun Neja Delta cewan su daina fasa bututun mai ko su fuskanci fushin ubangiji.
“Yakin da Tsagerun neja key i ba dai dai bane saboda yana cutar da zaman lafiyan kasa, man fetur kyauta ne da Ubangiji ya bamu kuma babu wanda ke da hakkin lalata shi” Yace
The post Gwamma Buhari da Jonathan – Dattawan Neja Delta appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us