Sports Betting

Trending

random

Dan kwallon Super Eagles ya sabunta kwantaragin sa da Chelsea

Dan wasan tawagar kungiyar kwallon kafa ta kasar Najeriya watau Super Eagles Kenneth Omeruo ya sabunta kwantaraginsa da kulob din Chelsea kamar yadda rahotanni suke zuwa mana.

Wakilin dan wasan dai Conleth Chika Akujobi shine ya shaidawa manema labaran kwallon kafa cewa yanzu dai dan wasan zai cigaba da zama dan kungiyar ta Chelsea har sai watan Juni na shekara ta 2019. A cewar sa “kungiyar Chelsea ita ce ta bukaci Kenneth din da ya kada wa’adin kwantaragin sa da su. Hakan kuwa akayi yanzu haka dai sai 2019 kwantaragin nasa zata kare.”

Mai karatu dai zai iya tuna cewa dan wasan ya koma kungiyar Chelsea ne a shekara ta 2012 bayan da ya wakilci najeriya gasar cin kofin duniya na yara matasa yan kasa da shekaru 20 a kasar Columbia. Haka zalika kuma dai kafin sabunta kwantaragin nasa da chelsea din da zata kare ne a shekara ta 2017.

Ana dai kuma kyautata zaton dan wasan zai je kungiyar Besiktas ne a matsayin dan aro a kakar wasa mai zuwa.

The post Dan kwallon Super Eagles ya sabunta kwantaragin sa da Chelsea appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Dan kwallon Super Eagles ya sabunta kwantaragin sa da Chelsea Reviewed by Olusola Bodunde on 16:29 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.