Sports Betting

Trending

random

Ibe zai kuma Bournemouth kan £15 miliyan

Jordan Ibe zai bar Liverpool ya koma Bournemouth

-Zai yi shekara 4 da kulop din a kan £15 milyan

Tuni ya wuce Amurka domin wurin sauran ‘yan wasan kulop din  

jordan-ibe  

Daya daga cikin kulop din da ke rukumin Premier na Britaniya Bournemoth, ya kammala sayen Jordan Ibe wani dan Najeriya da ke bugawa Liverpool kan Fam miliyan 15.

KU KARANTA:Manchester City shirye ta ke da ta saye Dan wasa Stones

Ana sa rai tsohon dan wasan gaban na Liverpool zai je ya taras da abokan wasan sa na sabon kulop din da ke Chicago a Amurka  inda suke yin atisaye gabannin kakar wasanni da za a shiga.

Shugaban Bournemouth Neill Blake ya ce “Muna matukar farin cikin kawo Jordan cikin mu saboda yana taka leda yadda ya kamata a Liverpool, kamar yadda idonmu ya nuna mana  a kakar wasannin da ta gabata, don haka mu na fatan ganin zarce haka a tare da mu domin ya na da faraga.”

KU KARANTA: An fitar da Kwallon da ta fi kowace kyau a Gasar EURO 2016

Ibe dan kasa da shekara 21 ya buga sau 41 a Liverpool kusan a duk karawar da kulop din ta yi a kakar wasannin ta wuce, ciki har da wasanni shida a gasar Europa a inda kulop din ya je har wasan karshe.

Tsohon dan wasan na Liverpool wanda kuma ya bugawa ‘yan kasa da shekara 21 na Ingila, ya sa rattaba hannu ne a kwatiragin shekara 5 a Antfield a watan Mayun shakarra nan, amma Jurgen Klopp ya ajiye a benchi.        

 

The post Ibe zai kuma Bournemouth kan £15 miliyan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Ibe zai kuma Bournemouth kan £15 miliyan Reviewed by Olusola Bodunde on 05:59 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.