Jam’iyyar APC ta kara yi ma Dino Melaye kaca-kaca
APC ta kara yi ma Dino Melaye kaca-kaca.
– Yan Jami’iyyar APC na Bangaren Kudu Maso Yamma sun kara yin suka game da kalaman Dino Melaye ga Sanata Oluremi Tinubu.
– ‘Ya ‘yan Jam’iyyar ta APC sun ce abin kunya ne ace mutum kamar Dino Melaye yana matsayin Sanata a Kasar nan.
– Jam’iyyar ta APC tace ta ma so ace ba Jam’iyya gida suke ba Dino Melaye.
– Ba mamaki Dino ya aikata abin da ya fadan Inji APC
Yan Jami’iyyar APC (Bangaren Kudu-Maso-Yamma) sun nuna mamakin su game da barazanar da aka ce Sanata Dino Melaye yayi ma Sanata ‘yar uwar sa, Oluremi Tinubu ta Legas. Jam’iyyar APC tace Dino Melaye yayi abin kunya. Sakataren Jam’iyyar na yankin Kudu-maso-Yammacin Kasar, Ayo Afolabi yayi tir da kalaman da Dino Melaye ya furta ga Sanata Tinubu. Jam’iyyar tayi Allah wadai Sanata Dino Melaye. Haka dai APC din ta ce Dino Melaye ba karamin abin kunya bane ga Majalisar Dattawar Kasar. Jaridar Vanguard ta dauko wannan rahoto.
KU KARANTA: RIKICIN JAM’IYYAR PDP NA TA KARA KAMARI
“Muna mamaki ace Sanatan Najeriya, na Majalisar dattawar Kasar nan zai yi irin wannan katobara domin zugar mulki. Shin ko Dino Melaye ya dauka Madam Tinubu sa’ar sa ce? Muna da masaniyar cewa Dino yayi yunkurin tsayawa takara a shekarar 2011, mutanen sa suka ce ba su yin sa. Sai a 2015 ya kama guguwar canji na APC ya dare mulki. Tun daga nan sai ya fara nuna asalin sa. Tir da wannan Sanata!” Sakataren Jam’iyyar na APC yayi wannan jawabi.
Jamiyyar dai ta bayyana cewa duk da haka ba za tayi mamaki ba har idan Dino Melaye yayi kokarin aikata abin ya fada na doke Sanata Tinubu. ‘Ya ‘yan jam’iyyar dai sun ce, sun yi takaicin ace Jam’iyyar su guda da Sanata Dino Melaye. Sun kira Shugaban Jami’iyyar na Kasa, John O. Oyegun da ya taka masa burki, kana Sufeta na ‘yan sandan Kasar ya binciki wannan lamari. Sai dai Dino Melaye ya karyata zargin fadan wasu kalaman batanci ga ‘yar uwar aikin sa.
The post Jam’iyyar APC ta kara yi ma Dino Melaye kaca-kaca appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us