Sharhin wasu jaridu na 27 ga watan Yuli
Yawancin jaridu na yau 27 ga watan Yuli sun mayar da hankalinsu ne a kan aringizon kasafin kudin shekara ta 2016 da ake zargin majalisar wakilai da aikatawa. Ga abin da wasun su ke cewa;
A cewar wani rahoto na jaridar The Nation batun zargin aringizon ya kara zurfafa a ranar Litinin 26 ga watan Yuli, a yayin da shugabancin majalisar ya nemi hukumar EFCC ta binciki Abdulmumini Jibrin tsohon shugaban kwamitin majalisar kan kasafin kudi.
Majalisar ta ce, binciken ya soma daga lokacin da jibrin ya ke shugaban kula da kudaden majalisar, Sai dai Jibrin ya ce an ki wayon, sai dai shugaban majalisar ya soma wanke kansa daga zargin hannu dumu-dumu a aringizon kasafin kudin tukunna.
KU KARANTA: ‘Yan majalisa sun caccaki Obasanjo kan furucinsa
A makon da ya gabata ne, korarren shugaban kwamitin, ya zargi shugaban majalisa Yakubu Dogara da matamakinsa Yusuff Lasun, da mai tsawatarwa Ado Doguwa, da kuma shugaban marasa rinjaye da Lee Ogor, da tilasta masa cusa ayyuka a mazabunsu na biliyan 40 a cikin ayyukan da Shugaban kasa ya gabatar za a yi na biliyan 100.
Amma a rahoton jaridar The Sun, wani dan majalisa ya tsegunta wani sakon wayar tes da Jibrin din ya aikawa abokan aikinsa, ya na rokonsu da cewa su taya shi kare aringizon kudaden da kwamitinsa ya yi.
KU KARANTA: A rika sara ana duban bakin gatari –Sanata Ali Ndume
A wani labari na jaridar The Punch, gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun kudiri aniyar ganin cewa ba ‘a tsige mataimakin shugaban majalisar dattijai Ekweremadu ba daga mukaminsa, wannan a cewar jaridar, shi ne yarjejeniyar da suka cimma a taron da suka yi da shugaban kasa a Abuja.
The post Sharhin wasu jaridu na 27 ga watan Yuli appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us