Ummaru Shinkafi ya rasu
– Allah yayi ma ummaru Shinkafi rasuwa
– Ya rasu ne a jiya bayan yayi fama da rashin lafiya
– Ya rasu ne a kasar Ingila.
Late Alhaji Umaru Shinkafi
Allah yayi ma Ummaru Shinkafi rasuwa a jiya. Ya rasu ne bayan yayi fama da matsananciyar rashin lafiya a kasar Ingila.
Ummar Shinkafi kafin rasuwar shi yayi aiki tare da yan sanda sirri na Najeriya daga 1979 zuwa 1983. Sannan kuma yayi ma Olu Falae mataimakin shugaban kasa a takarar zabe ta 199. Asalin shi dai dan Zamfara ne kuma kuma yana rike ta Sarautar Marafan Sakkwato.
Jaridar Premium Times ta bayyana cewa za’a dawo da gawar shi a ranar Juma’a inda za’a binne shi a Makabartar Abubakar na Ukku dake a Sakkwato.
Ya rasu ya bar mata Daya da Ya’ya 5. A cikin su akwai Zainab Baugud, wadda ita ce matar Gwamnan Jihar Kebbi, da kuma Aisha wadda itace matar Gwamnan Jihar Zamfara.
The post Ummaru Shinkafi ya rasu appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.
No comments:
Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us