Sports Betting

Trending

random

Dalilin aika Rundunar Sojoji zuwa Bayelsa-Sojin Najeriya

 

– Rundunar Sojin Kasar tace tana kokarin Najeriya ta zauna a matsayin Kasa guda.

– Domin martani ga masu kokarin kaddamar da Kasar Biafra ne aka tura Sojoji Jihar Bayelsa.

– Sojin sun bayyana cewa ba za a taba farar hula ko daya ba.

Soji

 

 

 

 

 

 

Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa ta tura rundunar ta zuwa Bayelsa ne domin masu kokarin tada-zaune-tsaye, an samu labarin cewa za a kaddamar da bude Kasar Jamhuriyar Biafra ko Niger-Delta Republic, hakan ya sa aka tura soji da kayan aiki zuwa bangaren Kasar na Bayelsa. Wasu tsageru masu suna ADAKI BORO sun gargadi Hausawa da yarbawa da ke yankin da su garzaya, su bar kasar kafin 1 ga watan Agusta. A farkon Agustan ne suka so su bude wannan kasa ta Neja-Delta. Wannan ne ya sa sojoji suka fantsama Garin Bayelsa, inda suka yi ta bincike, mutanen Garin Yenagoa da dama suka tsere zuwa kauyuka.

KU KARANTA: MU FA BA RUWAN MU DA NIGER DELTA AVENGERS, MUN TUBA

NAN ta rahoto cewa Sojin Kasar tana gudanar da aikin OPEARATION DELTA SAFE ne domin kawo zaman lafiya a yankin, Sojin Kasar sun yi alkawarin bin dokar Kasa da ka’idar gidan soja wajen harka da mutanen yankin da kuma tsageru. Rear Admiral J. Okojie, wanda shine mai jagoran tawagar Sojojin a Garin Yenagoa na Jihar Bayelsa ya bayyana cewa makaman da aka gani, duk cikin na aiki ne. Okojie yace Najeriya duk Kasar mu ce, muna da damar zagaya ko ina. Saboda haka OPEARATION DELTA SAFE zai tabbatar da zaman lafiya a wannan yankin, daga wasu masu neman bude wata Kasa cikin Najeriya, wanda ba zai yiwu ba.

Sojin dai sun yi alkawarin ba za su taba dan kowa ba, haka kuma za su bi ka’idoji wajen aiki, saboda haka babu dalilin tada hankali. Yanzu dai kungiyar ta janye batun kaddamar da sabuwar Jamhuriyyar ta Neja-Delta, sun bayyana cewa Tsohon Shugaba Jonathan ne ya tsaida su.

 

The post Dalilin aika Rundunar Sojoji zuwa Bayelsa-Sojin Najeriya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Dalilin aika Rundunar Sojoji zuwa Bayelsa-Sojin Najeriya Reviewed by Olusola Bodunde on 04:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.