Sports Betting

Trending

random

Makamai na yawo a Yankin Arewa da Neja-Deltan

 

– Majalisar dinkin duniya (UN) ta nuna cewa Najeriya na samun makamai masu dinbin yawa.

– Yan Kungiyar Boko Haram da Tsagerun Naja-Delta ke samun wadannan makamai.

– Hakan barazana ce ga harkar tsaron Kasar da kuma rayukar mutane.

UN MAKAMAI NAJERIYA

 

 

 

 

 

 

Majalisar dinkin duniya (Watau UN) ta nuna cewa Najeriya na nema ta zama wata matattarar makamai a yankin Afrika ta Yamma, inda makamai masu dinbin yawa suke yawo a cikin Kasar, musamman kuwa Arewacin Kasar inda Boko Haram suke da kuma yankin Neja-Deltan da ke a Kudanci masu fama da tsageru. Manyan makamai da bindigogi suna shiga hannun wadanda bai dace ba. Jaridar Vanguard ta rahoto cewa fiye da kashi 70% na makamai; kusan miliyan 500 da ke bangaren Nahiyar, to kusan miliyan 350 ba za su rasa alaka da Kasar Najeriya ba.

KU KARANTA: MANYAN LABARAI DAGA NAJERIYA

Olatokunbo Ige, wata darekta a UNREC; wata Hukuma a Karkashin Majalisar dinkin duniyan (UN) mai kokarin karbe makami da kuma wanzar da zaman lafiya a Afrika ya bada wannan jawabi a wani taro na PSSM wanda PRESCOM; Kwamitin Kasa da ke kula da harkar kananan makamai a Abuja. Darektar ta bayyana cewa makaman da aka fi sani da SALW; Watau kananan makaman barazana ne ga harkar tsaron Kasa da kuma rayukan jama’a gaba daya. Tace Najeriya tana daya daga cikin masu fama da wannan matsala ta kananan makami a hannu jama’a da dama, dalilin barkewar rikicin Kasar Libiya da Mali da kuma rikicin cikin Najeriya na Boko Haram a Arewa maso-Gabas da kuma Yankin Neja-Delta mai arzikin mai.

Darektar ta ce dole a duba wannan matsala, domin hakan zai kawo rashin cigaba a Kasar. Hakan ya sa Kungiyar EU take wannan aiki a Kasashe irin su: Burkina Faso, Chad, Mali, Mauritania, Niger da kuma najeriya domin karbe makami daga hannun bata-gari.

 

The post Makamai na yawo a Yankin Arewa da Neja-Deltan appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Makamai na yawo a Yankin Arewa da Neja-Deltan Reviewed by Olusola Bodunde on 04:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.