Sports Betting

Trending

random

Gwamnati ta tuna da Tsohon dan wasa Yekini

 

– Gwmnatin Jihar Kwara ta tuna da Tsohon dan kwallon Najeriya, Marigayi Yekini

– Kwamishinan wasanni na Jihar ya bayyana cewa Gwamnatin Kwara za ta kashe Naira Miliyan 30 wajen habaka harkar wasanni.

 – Kwamishina Bolakale Ayo ya bayyana cewa Jihar ba za ta manta da Marigayi Yekini ba.

KWARA SPORT COMMISSIONER

 

 

 

 

 

 

Kwamishinan matasa da wasanni na Jihar Kwara Bolalale Ayo ya bayyana kudirin Gwamnatin Jihar na tunawa da babban dan kwallon Najeriyan nan, Marigayi Rashidi Yekini, wanda ya rasu shekaru hudu da suka wuce. Da yake hira da NAIJ.com a Jiya Talata, 2 ga wannan watan, Ayo ya sanar da cewa Gwamnan Jihar ta Kwara zai bayyana shirin da ake yi na adana sunan Marigayi Yekini, Rashidi Yekini dai shine wanda ya fi kowa ci ma Najeriya kwallo a tarihi, Marigayi Yekini ya ci wa Super Eagles kwallaye har 37 duk shi kadai.

Kwamishina yana mai cewa: “Marigayi Yekini dan mu ne, dan wannan Jihar, rashin sa ba karamin abin takaici bane. Sai dai ba za mu manta da jarumi irin wannan va, mun shirya hanyar da za a bi wajen tunawa da Marigayi Yekini, kwanan nan, Gwamna Fatahi zai yi bayani game da wannan.” Mr. Bolalale Ayo yace: Abin da za muyi zai ba kowa mamaki, jama’a za su ga abin da wannan Gwamnati za tayi…” Kwamishinan dai ya kuma yo magana game da aikin da yayi bayan zuwan sa ofis, idan ba a manta ba, Mr. Kola Ayo ya canji Kwamishina Saheed Popoola ne a bayan nan.

KU KARANTA: KO WANENE KANU NWANKWO?

Jihar ta samo kudi har Naira miliyan 30 daga Bangaren Jakadancin Amerika da ke kula da cigaban sha’anin wasanni, don ganin an habaka wasanni a Jihar ta Kwara. Kwamishinan yayi alkawari za ayi amfani da kudin ta hanyar da ta dace. Sai dai duk da Kungiyar Kwara United ta sha kashi, inda har ta bar Gasar NPFL, kwamishinan yace kwanan za ta dago sama.

 

The post Gwamnati ta tuna da Tsohon dan wasa Yekini appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers 24/7.


Gwamnati ta tuna da Tsohon dan wasa Yekini Reviewed by Olusola Bodunde on 04:36 Rating: 5

No comments:

Thanks for reading, please share this post and leave a comment. Your comment is important to us

All Rights Reserved by Naija News Live © 2014 - 2015
Powered By Blogger, Designed by Sweetheme

Contact Form

Name

Email *

Message *

Powered by Blogger.